N29m: Tsohon Sanata Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Kudin Sanatoci Suka Yi Kadan

N29m: Tsohon Sanata Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Kudin Sanatoci Suka Yi Kadan

  • Sanata Ishaku Abbo ya fito ya kare kuɗin da ake biyan sanatocin da ke majalisar dattawa inda ya ce ba wasu kuɗi ba ne masu yawa
  • Tsohon sanatan ya ce idan aka kwatanta da tarin buƙatun da mutane ke kawowa wajen sanatoci, albashin na su bai taka kara ya karya ba
  • Ishaku Abbo ya bayyana cewa a lokacin da yake majalisa ana ba da N14.4m yayin da a yanzu ake ba da kusan N29m a kowane wata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo, ya bayyana cewa albashin sanatoci ba wasu kuɗi ba ne masu yawa.

Ishaku Abbo ya bayyana cewa albashin suna kawai ya tara idan aka kwatanta da tarin buƙatun da ke a ofishinsu.

Kara karanta wannan

Sabon ɗan Majalisar PDP da aka rantsar ya yi magana kan yiwuwar sauya sheka

Ishaku Abbo ya kare kudin da ake ba sanatoci
Ishaku Abbo ya ce kudin da ake ba sanatoci sun yi kadan Hoto: Senator Ishaku Abbo
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a ranar Lahadi, Ishaku Abbo ya bayyana cewa kuɗaɗen ba su isarsu yin ayyukan ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa ake biyan sanatoci duk wata?

Tsohon sanatan ya bayyana cewa albashi da alawus-alawus ɗinsa a lokacin da yake majalisa ya kai N14.4m, yayin da a yanzu sanatoci ke samun kuɗi har N29m.

"Lokacin da na ke majalisa, jimillar alawus ɗin shi ne N14.4m duk wata. Akwai alawus ɗin kaya, alawus na abin hawa da sauransu waɗanda duka idan aka haɗa za a samu N14.4m ciki har da albashin N1m a wata."
"Yanzu ya kusa N29m. Za a ga N29m kamar wasu kuɗi masu yawa, amma kuɗin ba wasu masu yawa ba ne. Ina faɗin wannan da zuciya ɗaya. Ba wai ina goyon bayan majalisa ba ne, amma zan faɗi gaskiya ne."

Kara karanta wannan

Kisan kiyashi: Yadda maƙabartun Gaza suka cika ana birne gawa kan gawa

- Ishaku Abbo

Tsohon sanatan ya nuna cewa tarin buƙatun da mutane suke kawowa wajen ƴan majalisa ya sanya kuɗin suka zama ba wani abu mai yawa ba, rahoton jaridar The Cable ya tabbaatar.

"Na talauce bayan shiga siyasa", Ishaku Abbo

Ishaku Abbo ya bayyana cewa ya talauce bayan ya bar kasuwancin da yake yi domin ya zama sanata.

"Na fi zama talaka a lokacin da na zama ɗan siyasa fiye da kafin na zama ɗan siyasa."

- Ishaku Abbo

Majalisa ta faɗi abin da ake biyan sanatoci

A wani labarin kuma kun ji cewa majalisar dattawa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da kuɗin alawus-alawus duk ƙarshen wata.

Majalisar dattawan ta musanta hakan ne a ranar Alhamis, biyo bayan kalaman da Sanata Kawu Sumaila ya yi na cewa yana samun kusan N22m duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng