"Ana Yi Mani Barazana": Ministan Tinubu Ya Koka Kan Kalubalen da Yake Fuskanta

"Ana Yi Mani Barazana": Ministan Tinubu Ya Koka Kan Kalubalen da Yake Fuskanta

  • Ministan makamashi na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa akwai masu yi masa barazana kan aikin da yake yi
  • Ministan ya bayyana yana samun barazanar daga mutanen da ke adawa da ci gaban da yake kawowa a ɓangaren wutar lantarki
  • Adebayo Adelabu ya ƙara da cewa a cikin ƙasa da shekara ɗaya da ya yi a ofis an ƙara ƙarfin lantarki 1,000MW da ƙasar nan ke samarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ya fuskanci barazana kan aikin da yake yi a ƙasar nan.

Ministan ya ce yana samun kiraye-kirayen barazana daga wasu ɓoyayyun mutane waɗanda ke adawa da ci gaban da ake samu a ɓangaren wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki matakin kawo karshen barayin man fetur a Najeriya

Adebayo Adelabu na fuskantar barazana
Ministan lantarki ya ce ana yi masa barazana Hoto: Hon. Adebayo Adelabu
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ce Adebayo Adelabu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a jihar Oyo yayin shirin ‘Political Circuit’ na tashar Fresh FM.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yiwa ministan Tinubu barazana

Ministan ya ce duk matsalolin da ake fuskanta a fannin wutar lantarki abu ne wanda za a iya magancewa.

"Za a samu turjiya, mutane za su yi ƙoƙarin kawo maka cikas, masu yin zagon ƙasa da sauransu. A karon farko bari na faɗi cewa na samu kiraye-kiraye na barazana."
"Ni ne ministan makamashi na 49 a Najeriya. Akwai yiwuwar sauran ministocin da suka gabace ni an hana su yin aikinsu yadda ya dace. Ba talakawa ba ne ke lalata turaken wutar lantarki da ababen fashewa."
"Laifi ne wanda aka tsara. Aiki ne na iyayen daba. Dukkaninmu ƴan Najeriya ne amma mun san abin da wasu daga cikinmu za su iya aikatawa."

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fayyace gaskiya kan wani sharri da aka dade ana yi masa

- Adebayo Adelabu

"Lantarkin Najeriya ta ƙaru", Adelabu

Da yake ƙarin haske game da gagarumin ci gaban da aka samu a shekara ɗaya da ya yi a kan kujerar minista, ya ce Najeriya da ƙyar take iya samar da wutar lantarki mai ƙarfin 4,000MW, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa cikin ƙasa da shekara da ya yi a ofis, tsare-tsaren da ya kawo sun sanya an samu ƙarin sama da 1,000MW.

Ministan makamashi ya yi albishir

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa yanzu wuta ta kara samuwa a sassan kasar nan biyo bayan shirin gwamnati.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanya wasu matakai da za su tabbatar da wadatar hasken wutar lantarki a ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng