Gwamnan Arewa Ya Shilla Kasar Waje Bayan Ya Dawo Hutun Kwanaki 30

Gwamnan Arewa Ya Shilla Kasar Waje Bayan Ya Dawo Hutun Kwanaki 30

  • Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya tafi ziyarar aiki ta kwanaki biyar zuwa ƙasar China
  • Gwamnan ya tafi ziyarar aikin ne bayan ya dawo daga hutun kwanaki 30 da ya tafi a cikin watan Yulin 2024
  • Gwamna Radda tare da tawagarsa za su tattauna da jami'an gwamnatin ƙasar China domin nemo hanyoyin zuba jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya koma bakin aiki bayan dawowa daga hutun wata ɗaya da ya tafi.

Gwamna Radda ya miƙa ragamar shugabancin jihar ga mataimakinsa Faruk Lawal sannan ya tafi hutun wata ɗaya a ranar 18 ga watan Yuli 2024.

Gwamna Radda ya tafi kasar China
Gwamna Dikko Radda ya tafi ziyarar aiki zuwa China Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Bayan dawowar gwamnan daga hutu, ya tafi ƙasar China domin ziyarar aiki ta kwanaki biyar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace kwamishina da matarsa a hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Radda ya tafi China?

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, ya bayyana maƙasuɗin ziyarar da gwamnan ya kai zuwa ƙasar China.

Wannan ziyarar aikin ita ce ta farko da Gwamna Radda ya yi tun bayan dawowarsa daga hutun wata ɗaya, wanda a lokacin mataimakin gwamna Mallam Faruk Lawal Jobe ya zama muƙaddashin gwamna."

"A ci gaba da ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na ƙulla ƙawance a duniya, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyar a ƙasar China."
"Gwamnan, tare da rakiyar manyan jami'an gwamnati, zai kasance a ƙasar daga ranar 18 zuwa 23 ga watan Agusta, 2024, domin lalubo hanyoyin zuba jari da ƙarfafa dangantaka."
"Gwamnan Radda ya samu tarba a filin jirgin sama na Daxing dake birnin Beijing, daga wajen William Lui, wanda zai karɓi baƙuncin tawagar a lokacin zamansu."

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

A cikin tawagar gwamnan akwai babban sakatarensa Abdullahi Turaji, kwamishinan noma da kiwo, Farfesa Ahmed Bakori, kwamishinan ciniki, kasuwanci da zuba jari, Adnan Habu da babban mai ba da shawara, Haroun Gana.

- Ibrahim Kaula Mohammed

Ana sa ran gwamnan da tawagarsa za su gana da jami'an gwamnatin ƙasar China, da masu zuba jari, da masana'antun sarrafa kayayyakin amfanin gona da na aikin gona daban-daban.

An gaji da yawon Gwamna Radda

Wani mazaunin jihar Katsina mai suna Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa waɗannan yawace-yawacen ba su ba ne abin da al'ummar jihar Katsina ke buƙata ba.

"Kusan mafi yawan lokuta waɗannan ziyarce-ziyarcen ba su haifar da wani ɗa mai ido. Mafi akasarin lokuta tarurrukan kawai suna kasancewa na shan shayi domin babu wani abu mai muhimmanci da yake biyo baya."
"Abin da muka fi buƙata shi ne gwamna ya zauna a jiha a nemo hanyoyin da za a kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da take ci mana tuwo a ƙwarya."

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

- Muhammad Auwal

Gwamnan Katsina ya yabawa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamantin jihar Katsina ta mika godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa karrama ƴaƴanta da muƙamai.

Muƙaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya yi godiya ga shugaban ƙasar a madadin gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng