Sule Lamido Ya Gano Matsalar da Ta Hana Najeriya Samun Ci Gaba
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan kiraye-kirayen da ake yi na a sauya kundin tsarin mulkin ƙasar nan
- Sule Lamido ya bayyana cewa matsalar ƙasar nan ta samo asali daga wajen shugabanni ba daga kundin tsarin mulki ba
- Ya nuna cewa masu aiwatar da kundin tsarin mulki ne suka jefa ƙasar nan halin da take ciki domin duk duniya babu inda ake da kundin tsarin mulki mara kura-kurai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ba shi ne matsalar Najeriya ba.
Sule Lamido ya bayyana cewa matsalar Najeriya ta samo asali ne daga shugabanninta.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kiran da ƙungiyar The Patriots, waɗanda suka ziyarci Shugaba Bola Tinubu tare da yin kiran a yi sabon kundin tsarin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya faɗi matsalar Najeriya
A wata hira da jaridar Thisday, Sule Lamido ya ce kura-kuran da ke tattare da aiwatar da kundin tsarin mulkin na 1999 na faruwa ne sakamakon kura-kurai na ɗan Adam, ba wai naƙasu da ke cikin kundin tsarin mulkin ba.
"Kundin tsarin mulki ba ya tunani kamar ƴan Adam. Ba ya ɗauke da mafitar kowacce daga matsalolinmu. Kamata ya yi ya zama ɗan jagora ba wai warware matsalolin ba."
"Mutanen da ya kamata su aiwatar da kundin tsarin mulkin ƴan Najeriya ne. Yanzu ku gaya min wanda ke yin abin da ya dace a Najeriya. Tun daga kan tashar motoci, makarantu har zuwa bankuna."
Saboda haka meyasa ake ƙoƙarin gujewa matsalar? Kundin tsarin mulki nawa muke buƙata kafin abubuwa su gyaru? Da matsala ta taso, sai mu ce a sauya kundin tsarin mulki. Kundin tsarin mulki nawa muke buƙata?"
"Domin haka komai yawan kundin tsarin mulkin da aka rubuta, indai har ba a gyara ba, ba zai yi aiki ba. Dubi ƙasar nan, mutane na faɗa da juna a kowane yanki. Shin wannan matsalar kundin tsarin mulkin ne ko ta masu aiwatar da shi."
"Ba matsalar kundin tsarin mulki ba ce, matsala ce ta masu aiwatar da shi. Duk duniya babu wani kundin tsarin mulkin da baya da kura-kurai."
- Sule Lamido
Sule Lamido ya caccaki gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya caccaki gwamnonin Arewa kan tafiyar da suka yi zuwa ƙasar Amurka.
Sule Lamido ya ce ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Amurka ta fallasa jahilcinsu ga kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.
Asali: Legit.ng