Yan Bindigar da Suka Sace Ɗaliban Jami'o'i 2 a Arewa Sun Turo Saƙo, Sun Faɗi Buƙatarsu

Yan Bindigar da Suka Sace Ɗaliban Jami'o'i 2 a Arewa Sun Turo Saƙo, Sun Faɗi Buƙatarsu

  • Masu garkuwa da ɗaliban likitanci 20 sun buƙaci a biya N50m a matsayin kuɗin fansa kafin su sake su
  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban jami'o'in Maiduguri da Jos a lokacin da suke kan hanyar zuwa taro a jihar Enugu da ke Kudu maso Gabas
  • Mataimakin shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya (NMA), Ushakuma Anenga ya ce su na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don ceto ɗaliban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da ɗaliban likitanci na Jami'ar Maiduguri da Jami'ar Jos sun fara tattauna da danginsu kuma sun nemi kuɗin fansa.

Mataimakin shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya (NMA) na biyu, Dakta Ushakuma Anenga, shi ne ya sanar da hakan ta wayar tarho. 

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsakiyar shagalin biki, sun tafka mummunar ɓarna

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun nemi N50m a matsayin kuɗin fansar ɗalibai 20 da suka yi garkuwa da su Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kamar yadda Leadership ta tattaro, masu garkuwan sun nemi a lalubo masu N50m a matsayin kuɗin fansar ɗaliban guda 20.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace ɗaliban

Idan baku manta ba a ranar Alhamis da ta gabata, wasu ƴan bindiga suka sace ɗalibai 20 da ke karantun likitanci a hanyarsu ta zuwa taron FECAMDS a Enugu.

Ɗalibai 12 sun fito ne daga jami'ar Jos da ke jihar Filato a Arewa ta Tsakiya yayin da ragowar ɗalibai takwas ɗin kuma sun fito ne daga jami'ar Maiduguri a Borno.

Da yake bayanin halin da ake ciki, Ushakuma Anenga ya ce ba zai yiwu su yi cikakken bayani ba saboda lamari ne da ya shafi tsaro.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Amma ya tabbatar da cewa kungiyar likitoci na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin ganin an kuɓutar da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

Anenga ya ce:

“Wannan lamari ne na tsaro, don haka ba za mu iya ba da cikakken bayani ba amma muna aiki kafada da kafada da dukkan hukumomin tsaro domin ganin an ceto su.
"Masu garkuwa sun ba ɗaliban wayar tarho kuma sun kira ƴan uwansu. A yanzu dai sun kira iyayensu, abokanan karatu da abokan arziki, muna fatan nan ba da jimawa za su kuɓuta."

Gwamma ya tallafawa waɗanda suka yi haɗari

A wani rahoton kuma gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya ware tallafin N30m ga waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a kauyen Dundaye.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta bai wa iyalan mutum biyar da suka rasu a haɗarin N15m yayin da waɗanda suka tsira kuma za a ba su N15m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262