Obasanjo Ya Fayyace Gaskiya Kan Wani Sharrin da Aka Dade Ana Yi Masa
- An daɗe ana cece-kuce game da batun cewa tatson tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya fito daga ƙabilar Igbo
- Wasu dai sun yi iƙirarin cewa mahaifin tsohon shugaban ƙasar haifaffen ƙabilar Igbo ne daga jihar Anambra a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- A karon farko Obasanjo ya mayar da martani inda ya bayyana iƙirarin a matsayin abin dariya sannan ya buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kawunansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - A karon farko tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya musanta shi ɗan ƙabilar Igbo ne, inda ya bayyana cewa lamarin yana ba shi dariya
Obasanjo ya ƙara da cewa, Najeriya ta dukkanin ƴan Najeriya ce ba tare da la’akari da bambancin al’adu ba.
Wasu dai sun daɗe suna zargin cewa mahaifin Obasanjo ya fito ne daga jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a lokacin da ake tunkarar zaɓen 2023, an zargi tsohon shugaban ƙasar da marawa Peter Obi na jam’iyyar Labour Party baya, saboda tatsonsa na Igbo.
Wane martani Obasanjo ya yi?
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta, Obasanjo ya yi tsokaci kan batun tsatsonsa na ƙabilar Igbo ne.
"Lamarin yana ba ni dariya."
- Olusegun Obasanjo
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar kasuwa ta Ndigbo Amaka a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Karanta wasu labaran kan Obasanjo
- Olusegun Obasanjo ya fadi hanyar da Najeriya za ta samu ci gaba
- "Gidan yari ya dace da su": Obasanjo ya koka kan halin shugabanni
- Obasanjo ya fito ya fadi gaskiya, ya bayyana babban kuskuren da Najeriya ta yi
Obasanjo ya fallasa ƴan majalisu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi ƴan majalisar dattawa da ta wakilai da ƙayyade albashinsu da kansu.
A cewar tsohon shugaban ƙasan, ƴan majalisar tarayya sun samu Naira miliyan 200 kowannensu, kuma sun sanya hannu sun karɓa.
Asali: Legit.ng