Farfesa Ya Hango Abin da Zai Tayar da Hankalin Tinubu, Ya Yi Gargadi
- Farfesa Toyin Falola na jam'iar Texas ya yi magana kan zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da aka yi a ƙasar nan
- Farfesan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai magance matsalolin da suka sanya mutane suka fito kan tituna
- Ya gargaɗi shugaban ƙasan kan ya ji tsoron aukuwar irin zanga-zangar da aka yi a ƙasar Bangladesh wacce ta sanya Firaministar ƙasar ta gudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shahararren farfesan tarihi, Toyin Falola, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza magance manyan matsalolin da suka haddasa zanga-zangar #EndBadBadGovernance.
Farfesan ya bayyana cewa Tinubu bai yi magana kan hanyoyin magance yunwa, tsadar rayuwa da rashin tsaro waɗanda su ne suka haifar da zanga-zangar ba.
Farfesa Toyin Falola na jami'ar Texas ya bayyana hakan ne a cikin shirin 'Inside Sources' na tashar Channels tv a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce masu zanga-zangar sun kyauta wajen sanar da zanga-zangar makonni kafin farawa domin ba gwamnati lokaci ta tsara dabarun magance rikicin da za a iya samu.
Wacce shawara farfesan ya ba Tinubu?
Farfesa Toyin Falola, ya ce kamata ya yi gwamnatin Tinubu ta ji tsoron zanga-zangar da ba za a iya shawo kanta ba kamar yadda aka yi a ƙasar Bangladesh.
"Lokacin da shugaban ƙasa ya yi jawabinsa, babu magana a kan tallafin man fetur, ababen more rayuwa, wutar lantarki da tsaro, waɗanda su ne suka sanya aka yi zanga-zangar.
"Martanin da ke fitowa daga fadar Aso Rock kawai shi ne 'ba mu son wani ya kawo cikas ga gwamnati.' Babu wanda yake son ya hargitsa gwamnati."
- Farfesa Toyin Falola
"Tinubu ya san akwai yunwa", Toyin
Ya bayyana babu yadda za a yi a ce Tinubu bai san yadda rayuwa ta yi tsada ba a Najeriya.
"Tinubu ya san halin da ake ciki, sannan ci gaba da neman uzuri ba shi ba ne hanyar gudanar da mulki. Amma daga ƙarshe mun yi sa'a ba a yi ɓarna ba. Mutane sun yi tsammanin faɗan Yarbawa da Igbo a Legas amma ba a yi ba."
"Abubuwan da suka sanya aka yi zanga-zangar ba a magance su ba. Abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai shi ne zanga-zanga wacce ba a shirya ba kuma ba a sanar ba, wannan ta fi hatsari."
"Saboda wannan ba za a iya yin komai a kanta ba. Wannan wacce aka yi an sanar wanda ya ba da dama aka samar da jami'an tsaro a kan hanya. Amma zanga-zangar da za a ji tsoro, ita ce irin ta Bangaladesh."
- Farfesa Toyin Falola
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren farko da Tinubu ya yi daga hawa mulkin Najeriya
- Dattijon kasa ya fadi yadda tallafin Tinubu ke jawo karuwar talauci
- Ana fargabar kitsa makarkashiya ga shirin tazarcen shugaba Tinubu a zaben 2027
Halin da Tinubu ya gaji tattalin arziƙi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta gaji tattalin arzikin ƙasa a cikin mawuyacin hali daga tsohon shugaba, Muhammadu Buhari.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya fadi haka ne yayin kaddamar da littafi mai suna 'gano siyasar tsare-tsaren ilimin bai daya na Najeriya.
Asali: Legit.ng