Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000

Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000

  • Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa jihar Nasarawa ba za ta iya biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi ba
  • Sule ya faɗi haka ne a wurin taronsa da ƴan kwadago kan walwalar ma'aikata wanda ya gudana a gidan gwamnati da ke Lafia
  • Gwamnan ya ce zai warware ƙarin girman da ba a yi ba tsakanin 2019 zuwa 2023 amma sabon albashi sai nan da shekara biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule ya ce jihar Nasarawa ba ta da ƙarfin tattalin arzikin da za ta biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamna Sule ya ce ko da jihar za ta iya aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 sai nan da shekaru biyu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamna Sule ya ce jihar Nasarawa ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi ba Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Asali: Facebook

Abdullahi Sule ya bayyana haka a wurin ganawarsa da wakilan ƙungiyar kwadago wanda ya gudanaa a gidan gwamnati da ke Lafia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Vanguard ta tattaro, taron ya maida hankali ne kan yadda za a inganta walwalar ma'aikatan gwamnati a jihar Nasarawa.

Gwamna Sule ya amince a farko?

Wannan kalamai da gwamnan ya ci karo da wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Peter Ahemba ya fitar cewa Nasarawa da dab da fara biyan albaahin N70,000.

Gwamnan ya shaidawa ƴan kwadagon cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin karawa ma'aikata girma wanda ba a yi ba a tsakanin 2019 zuwa 2023.

Sule ya ce:

"Ban manta da cewa fiye da watanni biyu da suka gabata mun amince za mu yiwa ma'aikata karin girma na tsakanin 2019 zuwa yau, wato daga 2019-2023.
"Ba za mu bari mu koma gidan jiya ba, irin wannan matsala da na gada, inda na taras da sama da shekaru takwas ba a yi wa ma’aikata karin girma ba.”

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya kare matakinsa na sukar Tinubu, ya yi jawabi mai kyau

Yaushe Nasarawa za ta biya N70,000?

Gwamna Sule ya amince da yiwa ma'aikata karin girma bayan da ƴan kwadago sun bukaci a dakatar da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na wani dan lokaci.

"A wancan lokaci na faɗa maku mu jira muka yadda za ta kaya game da ƙarin albashin. Yanzu mu ɗauko ya zo mana da ƙarin N800m, idan muka haɗa da N200 da muke biya ya zama N1bn.
"Kun ga jihar mu ba za ta iya biya ba, ba mu karfin tattalin arzikin da zamu iya biyan wannan adadi duk wata," in ji Sule.

Faɗan ƙarin albashi zai koma kan gwamnoni

Kuna da labarin Bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da N70,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata, ana bukatar gwamnoni su fara aiwatarwa

Kungiyar manyan ma'aikatan kasar nan (ASCSN) ta yi barazanar daukar mataki a kan gwamnatocin jihohi da su ka ki fara aiwatar da sabon albashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262