Miyagu Sun Nuna Karfin Hali, Sun Kashe Jami'in Gwamnati kusa da Gida a Nasarawa

Miyagu Sun Nuna Karfin Hali, Sun Kashe Jami'in Gwamnati kusa da Gida a Nasarawa

  • Daren Alhamis ya zo da mummunan al'amari a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa bayan yan ta'adda sun janye ma'aikacin gwamnati
  • Miyagun sun jira Hassan Yahaya mai shekaru 32 ya dawo daga aiki, sannan su ka fitar da shi da karfin tsiya daga motarsa, su ka yi tafiyarsu
  • Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi alhinin rashin imanin da miyagun su ka tafka, ta dauki alkawarin tabbatar an hukunta yan ta'addan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Nasarawa - Mazauna angwan mai matasa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa sun kwana da takaicin kisan wani matashin jami'in gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta hana amfani da lasifika a masallatai da coci, an kafawa masu ibada sharadi

An samu labarin cewa miyagun sun jira shugaban kula da shirin Fadama III na gwamnatin jiha, Hassan Yahaya a kofar gidansa, ya na isowa su ka tafi da shi.

Nasarawa State Government
Miyagu sun kashe jami'in gwamnatin Nasarawa har gida Hoto: Nasarawa State Government
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa miyagun ba su yi nisa da gidan matashin mai shekaru 32 ba, suka kashe shi tare da tafiya da wasu sassan jikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar ta bayyana marigayin a matsayin mai riko da aiki dai-dai gwargwado, kuma za a yi kewarsa.

Gwamnatin Nasarawa ta yi tir da kisan

Gwamnatin Abdullahi Sule ta jihar Nasarawa ta yi Allah wadai da kisan daya daga cikin jami'inta da miyagu su ka yi har gida.

A sakon ta'aziyya da babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Addra ya fitar, gwamnati za ta tabbata an kamo miyagun.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince miyagu su na aikata abin da su ka ga dama a jihar ba, tare da addu'ar Allah ya saka masa da aljannatul Firdausi.

Kara karanta wannan

Direban adaidaita sahu ya maida jakar kudin da ya tsinta, yan sanda sun sa cigiya

Yan daba sun yi barna a Nasarawa

A wani labarin kun ji yadda karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa ta fuskanci tashe-tashen hankula daga 'yan daba yayin da ake adawa da manufofin Tinubu.

Shugaban karamar hukumar Karu, Thomas James da ya yi karin bayani ya ce an sanya dokar hana zirga-zirga na wani lokaci domin dakile bazuwar rashin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.