"Kasar Mu ce Duka," Cif Obasanjo Ya Yi Barkwanci kan Zargin Asalinsa Ibo ne

"Kasar Mu ce Duka," Cif Obasanjo Ya Yi Barkwanci kan Zargin Asalinsa Ibo ne

  • Tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana matsayarsa kan nuna wariya ga wata kabila a Najeriya
  • Obasanjo,wanda ya karbi bakuncin kungiyar yan kasuwa ta Ndigbo Amaka ya ce kowanne dan kasa na da hakki a cikinta
  • Kan zargin da ake yi na cewa mahaifinsa dan kabilar Ibo ne, Cif Olusegun Obasanjo ya ce abin kan ba shi dariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun - Tsohon shugaban kasa,Cif Olusegun Obasanjo ya ce ba ya goyon bayan ware wata kabila ko korarsu daga Najeriya.

Cif Obasanjo ya shaidawa kungiyar Ndigbo Amaka Progressive Market Association cewa haka kuma ba ya goyon bayan korar wata kabila daga wani bangare na kasar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Obasanjo
Cif Obasanjo ya nuna rashin goyon bayan korar wasu kabilu daga sassan kasa Hoto: Olusegun Obasanjo Quotes
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a sanarwar da hadimin tsohon shugaban kan yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya ce Hausawa, Yarbawa da Ibo sun yi yaki tare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sun yi yadin tabbatar da hadin kansu, saboda haka duk wanda ya ce a sallami wata kabila, shi ne ya kamata ya bar kasar baki daya.

"Ina dariya" Obasanjo kan alaka da Ibo

Tsohon shugaban kasar nan, Cif Obasanjo ya tabbatar da cewa ya kan samu labarin zargin da ake na cewa mahaifinsa dan kabilar Ibo ne.

Obasanjo ya bayyana cewa duk lokacin da ya ji irin wannan hasashe na jama'a, abin kan ba shi dariya sosai, kamar yadda Jaridar Leadership ta wallafa.

Sai dai Cif Obasanjo bai kara cewa uffan kan sahihancin zargin da ake ta yamaɗiɗi da shi kan asalinsa na kabilar Ibo ba ne.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Olusegun Obasanjo ya taso Tinubu a gaba

A baya mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce duk da akwai manufofin gwamnatin Bola Tinubu da dole sai an aiwatar da su, amma an yi gaggawa.

Cif Obasanjo ya dora aikin lalacewar tattalin arzikin Najeriya da ake gani a yanzu kan gwamnatin APC mai ci ta Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon shugaban ya ce cire tallafin fetur da mayar da musayar Dala kan tsarin bai daya abu ne da ya kamata, amma an yi su cike da kura-kurai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.