Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Kadu, An Gano Dalilan Karuwar Asarar Rayuka

Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Kadu, An Gano Dalilan Karuwar Asarar Rayuka

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana rashin jin dadin yadda ake samun rasa rayuka a jihar, tare da cewa ana daukar matakai
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka, ya ce akwai dalilai da dama da ke jawo asarar rayukan
  • Kwamishinan ya roki mazauna Kano da kar su boye bayanai, a rika gaggawar sanar da su domin su dauki matakan ceto jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda ta kasa, reshen jihar Kano ta ce akwai damuwa matuka kan yadda ake samun karuwar mace-mace a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Kara karanta wannan

Arangama tsakanin manoma da makiyaya ta jawo asarar rayuka a Adamawa

Salman
Rundunar yan sandan Kano ta ce ana samun karuwar mace-mace a jihar Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

A sakon da SP Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwamishina Dogo ya ce dole jama'ar Kano su fara daukar matakan kare rayukansu a mu'amalarsu ta yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan rasa rayuka a jihar Kano

Rundunar yan sandan Kano ta bankado dalilan samun rasa rayuka a jihar, Jaridar Vanguard ta tattaro.

Daga cikin dalilan da aka bayyana akwai kisan kai ta hanyar sukar wuka, kwalabe da sauran makamai a wasu sassan jihar.

Kwamishinan 'yan sanda, Salman Dogo ya kuma ce ana samun karuwar rasa rayuka saboda ambaliyar ruwa bayan shafe akalla kwanaki shida ana zabga ruwan sama.

Yan sandan Kano sun roki jama'a

Rundunar yan sandan Kano ta roki mazauna jihar su taimaka mata da bayanan da za su tallafa mata wajen dakile asarar rayuka.

Rundunar ta bayyana cewa za a iya tuntubarta ta lambobin kar ta kwana da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun wargaza kotu a Kano, sun jawo asarar N1bn yayin zanga zanga

Yan sandan Kano sun mika matasa Abuja

A baya kun samu labarin yadda rundunar yan sandan Kano ta mika wadanda ake zargi da daga tutar Rasha yayin zanga-zangar adawa da gwamnati zuwa Abuja.

Rundunar ta bayyana haka ne bayan jaddada matsayarta na cewa babu mutumin da ya rasa ransa yayin zanga-zanga duk da hujjar da ke nuna akasin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.