Ba a Gama Farfadowa ba, An Shirya Gudanar da Sabuwar Zanga Zanga a Najeriya

Ba a Gama Farfadowa ba, An Shirya Gudanar da Sabuwar Zanga Zanga a Najeriya

  • Ƙungiyar CSNOESA ta shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da kamfanin NNPCL da mahukuntansa kan ƙarancin fetur
  • CSNOESA da za ta gudanar da zanga-zangar a birnin Abuja, ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari
  • Ta koka kan riƙon sakainar kashi da shugaban na NNPCL watau Mele Kyari yake yi kan batun gyaran matatun man fetur huɗu na ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Civil Society Network on Economic and Social Advancement (CSNOESA) ta ce tana shirin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kamfanin NNPCL da mahukuntansa.

Ƙungiyar CSNOESA za ta gudanar da zanga-zangar ne kan ci gaba da samun matsalolin da ake yi a ɓangaren man fetur.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi hanyar da za a iya raba Tinubu da mulkin Najeriya

Za a yi zanga-zanga a Abuja
Kungiyar CSNOESA za ta yi zanga-zanga a Abuja Hoto: NurPhoto
Asali: Twitter

Meyasa za a yi zanga-zangar?

Daily Trust ta ce da yake magana a wani taron manema labarai jiya a Abuja, kakakin ƙungiyar na ƙasa, Abubakar Yale, ya ce za su gudanar da zanga-zangar ne domin kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da harkokin man fetur a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Yale ya bayyana shirin ƙungiyar na mamaye hedikwatar NNPCL a ranar 22 ga watan Agusta, 2024, har sai Shugaba Bola Tinubu ya tsige shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.

Ana rokon mutane su fito zanga-zanga

Kakakin na CSNOESA ya buƙaci ƴan Najeriya da su fito su shiga zanga-zangar ta lumana, inda ya jaddada cewa tana da muhimmanci ga makomar ƙasar nan domin ganin an kawar da ɓata gari, rahoton Peoples Daily ya tabbatar.

"Mun damu matuka game da matsalar ƙarancin man fetur da ƙasar nan ke fuskanta sakamakon gazawar kamfanin NNPCL. Ana sayar da man fetur a kan N1,500 a wajen ƴan bumburutu a wasu sassan Najeriya ciki har da Abuja."

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

"Abin takaici ne wanda ba ya misaltuwa da tsabar mugunta cewa Mele Kyari da gangan ya ƙi bari matatun man fetur huɗu na ƙasar nan su yi aiki."
"A ranarsa ta farko ta fara aiki shekara huɗu da suka gabata, ya yi alƙawarin cewa kafin ƙarshen wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, matatun za su yi aiki."
"Yanzu bayan shekara huɗu, ko guda ɗaya ba ta fara aiki ba. Mele Kyari ya yi matuƙar gazawa."

- Abubakar Yale

NNPCL ya magantu kan ƙarancin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ƙarancin man fetur da ake fama da shi ya samo asali ne sakamakon cikas a ayyukan wasu jiragen mai guda biyu.

A cewar kamfanin na NNPCL, matsalar da jiragen ruwan masu ɗauke da fetur din suka samu ya haifar da tangarda wajen samar da mai da kuma rarraba shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng