Matatar Man Dangote Ta Fadi Lokacin Fara Fitar da Man Fetur Zuwa Kasuwa

Matatar Man Dangote Ta Fadi Lokacin Fara Fitar da Man Fetur Zuwa Kasuwa

  • Matatar man Dangote ta sake ba da tabbacin cewa lokacin da za ta fara fitar da man fetur zuwa kasuwa na watan Agusta na nan daram
  • Shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya musanta cewa an ƙara ɗage lokacin fara fita da man fetur
  • A ba ya dai matatar ta Dangote ta sha sanya lokacin fara fitar da man fetur ɗin, amma sai ta zo ta ɗage daga baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Matatar man Dangote ta ce za ta fara samar da man fetur a cikin watan Agusta.

Wasu rahotanni sun yi iƙirarin cewa an dage ranar da matarar za ta fara fitar da man fetur zuwa kasuwa.

Kara karanta wannan

Katsina: Gwamna ya sauya dokar da ya sanya lokacin zanga zanga a Najeriya

Dangote ya fadi lokacin fara samar da man fetur
Matatar man Dangote ta ce za ta fara samar da man fetur a watan Agusta Hoto: Bloomberg, Contributor
Asali: UGC

Yaushe matatar Dangote za ta fitar da fetur?

Da yake magana da jaridar TheCable a ranar Laraba, shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya ce rahotannin ɗage lokacin ƙarya ne. 

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chiejina ya ce matatar man tana kan hanyar fara samar da man fetur a cikin watan Agusta kamar yadda aka tsara, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Chiejina ya buƙaci jama’a da su daina ɗaukar jita-jita, yana mai cewa kamfanin yana da hanyoyin fitar da bayanai ga abokan hulɗarsa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran za a fara samar da man fetur daga matatar ta Dangote a wannan watan na Agusta.

Matatar Dangote ta saba ɗage lokaci

A ranar 18 ga watan Mayu, Aliko Dangote, ya ce daga watan Yuni, matatar za ta fara samar da man fetur, inda ya ƙara da cewa Najeriya ba za ta sake shigo da shi daga ƙasashen waje ba.

Kara karanta wannan

Matatar man Dangote za ta sayar da litar fetur a kan N600? Kamfanin ya yi karin haske

A watan Yuni, hamshakin ɗan kasuwar ya ce saboda wani ɗan jinkiri da aka samu, matatar man za ta fara samar da man fetur a watan Yuli.

Sai dai a ranar 15 ga watan Yuli, matatar Dangote ta ƙara ɗage lokacin samar da man fetur zuwa watan Agusta.

Har ila yau, a ranar Talata, matatar ta ce ba ta ƙayyade farashin man fetur a kan N600 kan kowace lita ba kafin lokacin da zai shiga kasuwa.

Atiku ya magantu kan matatar Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin da ake yi na ganin bayan matatar man Dangote da gangan.

Atiku ya bayyana cewa matatar man Dangote za ta iya warware matsalar ƙarancin man da ake fama da ita a ƙasar nan da samar da isassun kuɗaɗen ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta dauki matakin saukakawa mutane kan dokar hana fita

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng