Jami'an 'Yan Sanda 181 Sun Samu Karin Girma a Kano, Kwamishina Ya Ja Hankalinsu
- Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya yi wa jami'ai 181 da suka samu ƙarin girma ado da sababbin igiyoyinsu
- Salman Dogo Garba ya buƙace su da su ƙara zage damtse wajen yaƙi da miyagun laifuka da masu aikata su a jihar
- Jami'an waɗanda suka samu ƙarin girman daga sufeto zuwa mataimakin sufeto (ASP II) sun kuma samu saƙon taya murna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwamishinan ƴan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya yi wa jami’ai 181 da aka yi wa ƙarin girma ado da sababbin igiyoyinsu.
Salman Dogo Garba ya kuma yi kira gare su da su ƙara himma wajen yaƙi da miyagun laifuka a jihar.
Ƴan sanda sun samu ƙarin girma a Kano
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Laraba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, manyan jami’an da aka ƙara musu girma daga sufeto zuwa mataimakin sufeto (ASP II) na daga cikin waɗanda hukumar ƴan sanda ta yi wa ƙarin girma a ranar 29 ga watan Yuli, 2024.
"A ranar 13 ga watan Agusta, 2024, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya sanyawa manyan jami’an ƴan sanda 181 da aka yiwa ƙarin girma sababbin igiyoyinsu."
- ASP Abdullahi Haruna
Kwamishina ya ta ya su murna
A nasa jawabin, kwamishinan ƴan sandan ya taya jami'an da suka samu ƙarin girman da iyalansu murna, inda ya jaddada muhimmancin jajircewa, ƙwarewa, da nuna nagarta wajen samun ƙarin girma.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga sufeto janar na ƴan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, da hukumar ƴan sanda ta ƙasa.
Ƴan sandan Kano sun magantu kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Kano ta hakikance kan cewar babu mutumin da harbin bindiga ya yi sanadiyyar rasuwarsa yayin zanga zanga.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Salman-Dogo Garba ne ya bayyana haka ga manema labarai a zantawarsa da su a ofishin 'yan sandan Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng