Zargin Ta'addanci: Kotu Ta ba EFCC Umarnin Rufe Miliyoyin Daloli a Asusun 'Yan Kirifto
- Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta zargi wasu 'yan kasar nan da amfani da hanyar kirifto wajen daukar nauyin ta'addanci
- Wannan ya sanya hukumar ta garzaya kotu ta ne neman izinin wasu daga cikin asusun kirifton da ta ke zargi da halasta kudin haram
- EFCC ta yi nasara, domin kotun da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta amince hukumar ta rufe wasu asusun mutane guda hudu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sahalewa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta rufe asusun kirifton wasu mutane hudu.
Hukumar EFCC na zargin masu asusun da daukar nauyin ta'addanci da halasta kudin haram, da kuma daukar nauyin zanga-zanga a kasar nan.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa Mai Shari'a Emeka Nwite ya amince a rufe asusun kirifton hudu da ke dauke da Dala Miliyan 37,061,867,869.3.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta za ta rufe asusun kirifto
Da hukuncin da Mai Shari'a Nwite ya aiwatar, hukumar EFCC za ta samu damar rufe manyan asusun kirifto da ta ke zargi da rashin gaskiya guda hudu, Jaridar Premium Times ta tattaro.
Yanzu, EFCC za ta rufe asusu na farko wanda ke dauke da Dala Miliyan 37 million, sai sauran asusun mai dauke da Dala 967, akwai mai Dala 90 da Dala 443,512.37.
Sai dai hukumar yaki da cin hancin ba ta bayyana sunayen wadanda ake zargin sun mallaki asusun kirifton ba, amma ta ce an gano su na da hannu a cikin zanga-zangar adawa da Tinubu.
EFCC na samun nasara kan masu cin hanci
A baya mun ruwaito cewa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta samu gagarumar nasara a yakin da ta ke da masu yiwa arzikin kasar nan barna.
Hukumar ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato N232bn da $70m a tsakanin watan Mayun 2023 zuwa watan shekarar 2024, tare da kwato wasu kudin daga kasashen waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng