Dan Bello Ya Sake Kwancewa Gwamnatin Tinubu Zani a Kasuwa
- Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fito ya ƙara yi wa shugaba Bola Tinubu wankin babban bargo
- Dan Bello ya bayyana cewa ƴan Najeriya na fama da yunwa saboda tsare-tsaren da gwamnati mai ci ta kawo
- Ya ƙalubalanci gwamnati da ta shigar da shi ƙara a kotu idan har ba ta jin daɗin wayar da kan jama'an da yake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Bello Habib Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya sake caccakar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Dan Bello ya bayyana cewa yunwa na kashe ƴan Najeriya saboda manufofin Shugaba Bola Tinubu.
Dan Bello ya ƙalubalanci gwamnati
Dan Bello ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Trust tv a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙalubalanci gwamnati da ta shigar da ƙara a kansa idan har ba ta jin daɗin yadda yake ƙware mata zani a kasuwa.
Dan Bello ya ce ba ya da alaƙa da wata jam’iyyar siyasa a ƙasar, yana mai cewa babu wanda yake yiwa aiki, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Me Dan Bello ya ce kan gwamnatin Tinubu?
"Idan har abin da na ke yi bai yi musu daɗi ba, hakan na nufin jama'a na jin daɗinsa. Idan abin da suke yi mai kyau ne babu wanda zai ji cewa bidiyoyin da na ke yi suna taka wata rawa."
"Hakan na nufin cewa ba su yin ƙoƙarin da ya dace. Abin da suke yi duk shi ya jawo wannan matsalolin da muke fuskanta."
"Jam'iyya mai mulki ta kawo tsare-tsare da suka jefa mutane cikin yunwa. Mutane na mutuwa. Mutane yanzu na cin ciyawa. Mutane na shan gurɓataccen ruwa. Mutane na zuwa suna cewa ba su ci abinci ba na tsawon kwana uku."
"Wannan ba annoba ba ce ta ruwan sama ko iska mai ƙarfi. Hakan ya auku ne saboda wasu tsare-tsare waɗanda za a iya kauce musu. Waɗannan shugabannin kawai sun kawo tsare-tsare sannan sun toshe kunnuwansu."
"Yanzu ba su jin daɗi saboda suna samun biliyoyin kuɗi ta hanyar yin gurɓatattun ayyuka. Eh ina son su ƙi jin daɗin, ina son su je kotu. Ina son su shigar da ƙara, su yi duk abin da za su iya domin mu yi shiru. Hakan ya nuna cewa aikinmu na yin kyau."
- Bello Habib Galadanci
Yaron El-Rufai ya ba Dan Bello shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Bashir Nasir El-Rufai ya yi kira ga Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello kan bidiyoyin da yake yi.
Yaron na tsohon gwamnan jihar Kaduna ya faɗawa Bello Habib Galadanci ya yi hattara da yadda yake fitar da bidiyoyi da ƙoƙarin faɗakar da al’umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng