"Yana da Kyakkyawan Shiri": Hadimin Tinubu Ya Kwantar da Hankalin Matasan Najeriya
- Babban mataimaki na musamman ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin ɗalibai ya buƙaci matasa da su ƙara kai zuciya nesa
- Asefon Sunday ya buƙaci matasan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu domin yana da kyakkyawan shiri a kansu
- Hadimin na shugaban ƙasan ya buƙaci matasan da kada su bari wasu maƙiyan ƙasar nan su yi amfani da su domin cimma wata buƙata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ɗalibai, Asefon Sunday, ya tunatar da matasa shirin Shugaba Bola Tinubu a kansu
Hadimin na Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya da su ƙara haƙuri da wannan gwamnati mai ci.
Hadimin Bola Tinubu ya roƙi matasan Najeriya
Asefon Sunday ya yi wannan roƙo ne a garin Makurdi a lokacin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zanta da maneman labaran ne yayin wani shirin horar da wasu shugabannin ƙungiyoyin ɗalibai na manyan makarantu na tsawon kwanaki uku.
Shirin ba da horon, mai taken, ‘Gina shugabannin matasa masu kishin ci gaban ƙasa’, ya samu mahalarta daga yankin Arewa ta tsakiya.
Shirin gwamnatin Tinubu kan matasa
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawan shiri kan matasa sannan ya buƙace su da kada su bari a yi amfani wajen kawo hargitsi a ƙasar nan, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Ina kira ga matasa da su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda yana da kyakkyawan shiri a kansu."
"Ka da su bari maƙiyan ƙasar nan su yi amfani da su saboda akwai mutane da dama waɗanda tsare-tsaren wannan gwamnatin ba su yi daidai da ra'ayinsu ba.
"Waɗanda suka kwashe arziƙin ƙasar nan su ne suke son yin amfani da matasa da ɗalibai domin yin zanga-zangar da za ta kawo cikas ga gwamnati."
- Asefon Sunday
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- Shugaba Tinubu ya tsawaita wanda Buhari ya ba mukami a gwamnatinsa
- Tinubu ya kawo doka a harkar lafiya, likitoci za su daina tafiya ketare
- Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu kan batun canza tsarin mulkin Najeriya
Jigon APC ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC, Jesutega Onokpasa, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara kan hanyar gyara Najeriya.
Jesutega ya shawarci Tinubu da ya samar da ƙwararrun ƴan Najeriya a kusa da shi domin ya samu damar gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi da kuma cimma tsare-tsarensa kan tattalin arziƙin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng