Gwamnan Bauchi Ya Mika Muhimmiyar Bukata Gaban Majalisa Bayan Gama Zanga Zanga
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya shirya maye gurbin kwamishinoni uku a gwamnatinsa
- Gwamnan ya mika sunayen mutum uku ga majalisar dokokin jihar domin ta amince da su a matsayin sababbin kwamishinoni
- Biyu daga cikin kwamishinonin da za a maye gurbinsu, sun yi murabus domin takara a zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya miƙa sabuwar buƙata a gaban majalisar dokokin jihar.
Gwamna Bala ya aika da buƙatar tabbatar da mutane uku a matsayin kwamishinoni a gwamnatinsa.
Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Agusta, 2024, na ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kashim, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wanene sababbin kwamishiononin?
Sunayen da aka miƙa domin amincewa da su sune Injiniya Mohammed Binni Abdulkadir daga ƙaramar hukumar Itas/Gadau wanda ya maye gurbin Honorabul Hajara Jibrin Gidado, wacce ta yi murabus kwanan nan.
Hajara Gidado ta yi murabus daga muƙaminta na kwamishina domin yin takarar zama shugabar ƙaramar hukumarta a zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Mutum na biyun shi ne Honarabul Sani Mohammed Dambam daga ƙaramar hukumar Dambam, wanda zai maye gurbin marigayi Honorabul Ahmed Aliyu Jalam.
Marigayi Ahmed Aliyu Jalam ya rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi watanni biyu da suka gabata a hanyarsa ta zuwa Potiskum a jihar Yobe domin ganawa da iyalansa.
Mutum ta uku cikin waɗanda gwamnan ya buƙaci a amince da su, ita ce Honarabul Zainab Baban Takko daga ƙaramar hukumar Bauchi, wacce za ta maye gurbin Honarabul Mahmood Babamaji, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa.
Mahmood Babamaji ya yi murabus ne domin yin takarar shugaban ƙaramar hukuma a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
Gwamnan Bauchi ya ba gwamnonin Arewa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan zanga-zangar yunwa da aka yi a faɗin ƙasar nan.
Gwamna Bala ya bayyana cewa zanga-zangar hannunka mai sanda ce a gare shi da sauran gwamnonin Arewacin Najeriya kan su tashi wajen samar da shugabanci mai kyau a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng