Bayan Gama Zanga Zanga, Gwamna a Arewa Ya Ɗauko Hanyar Share Hawayen Talakawa

Bayan Gama Zanga Zanga, Gwamna a Arewa Ya Ɗauko Hanyar Share Hawayen Talakawa

  • Gwamnatin jihar Neja karƙashin jagoranci Muhammed Umaru Bago ta yi alkawarin bullo da shirye-shiryen ragewa mutane radaɗin rayuwa
  • Muƙaddashin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba ya yabawa masu ruwa da tsaki, ƴan jihar Neja bisa yadda suka tsame kansu daga zanga-zanga
  • Garba ya ce gwamnatin Neja za ta yi iya bakin kokarinta wajen magance wahalhalun da mutane ciki ta hanyar sababbin shirye-shiryen tallafi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - A karon farko bayan kammala zanga-zanga, gwamnatin jihar Neja karkashin Gwamna Umaru Bago ta yi alkawarin sharewa talakawanta hawaye.

Muƙaddashin gwamna, Kwamared Yakubu Garba ya ce gwamnati za ta kirkiro shirye-shirye na musamman da za su ragewa mutane raɗaɗi a wannan hali da ake ciki.

Kara karanta wannan

An gano mutane 19 da suka mutu sakamakon mummunan haɗarin jirgi

Muhammad Umar Bago.
Zanga-zanga: Gwamnatin Neja ta yi alkawarin yakar tsadar rayuwa Hoto: Muhammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Gwamnatin Neja ta ji koken talakawa

Yakubu Garba da bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa al'ummar Neja kai tsaye kan batutuwan da suka taso bayan zanga-zangar da aka yi, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jinjinawa masu ruwa da tsaki da mazauna jihar bisa yadda suka kame kansu daga shiga zanga-zangar da aka yi kwanan nan, suka zaɓi zaman tattaunawa.

Matakan da gwamnatin Niger ta ɗauka

Muƙaddashin gwamnan ya yi nuni da cewa tattaunawa da fahimtar juna su ne ginshikin magance duka wasu rikice-rikice da kuma ciyar da jihar zuwa gaba.

Yakubu Garba ya tabbatar da cewa gwamnatin Muhammed Umar Bago ta himmatu matuka wajen kyautata walwala da jin dadin al'ummar jihar.

Ya ƙara da cewa tsare-tsare irin na sayar da hatsi a farashi mai rangwamen kashi 50% a duka kananan hukumomi 25 na cikin kokarin da ake yi na tallafa wa mutane su rage raɗaɗi.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

Gwamnatin Neja za ta bullo da shirin tallafi

Yakubu ya ce:

"Za mu yi iya bakin kokarin mu wajen tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali da walwala a fuskokin al'umma, nan ba da jimawa za mu kawo shirye-shiryen da za su amfani al'umma."

Ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hada kai da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke addabar jihar Neja da kasa baki daya.

Kotu ta yanke hukunci kan zanga-zanga

A wani rahoton kuma ministan babbar birnin tarayya Abuja ya yi nasara a bukatar da ya shigar gaban kotu kan masu zanga-zangar tsadar rayuwa.

Alkalin ya amince da bukatar Nyesom Wike na tsawaita umarnin taƙaita zanga-zanga a filin wasa na ƙasa MKO Abiola maimakon a hau tituna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262