Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Matakin Saukakawa Mutane kan Dokar Hana Fita
- Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, ta cire dokar hana fita da ta sanya a ƙananan hukumomi takwas na jihar
- Dokar hana fitan da aka sanya sakamakon rikicin da aka samu a lokacin zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci, yanzu an cire ta gaba ɗaya
- Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar, Sagir Musa, ya ce yanzu jama'a za su iya fitowa su gudanar da harkokinsu ba tare da wata takura ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ɗage dokar hana fita da ta sanya a ƙananan hukumomi takwas na jihar.
Gwamnatin ta sanya dokar ne sakamakon rikicin da aka samu a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance.
Gwamnatin Jigawa ta cire dokar hana fita
Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar, Honorabul Sagir Musa ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan taron tsaro na jihar wanda Gwamna Umar Namadi ya jagoranta, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko an sassauta dokar hana fitan daga ƙarfe 5:00 na safe zuwa ƙarfe 9:00 na dare a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa.
Ƙananan hukumomin su ne Dutse, Kazaure, Gumel, Hadejia, Kiyawa, Birnin kudu, Babura, da Roni.
Meyasa aka cire dokar hana fitar?
Sagir Musa ya ce matakin ya biyo bayan sake duba yanayin tsaro a ƙananan hukumomin da abin ya shafa, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ya ce bisa ɗaukar wannan matakin, yanzu jama'a na iya gudanar da harkokinsu cikin walwala ba tare da wata takura ba.
Sai dai ya buƙaci al’ummar jihar da su kiyaye doka da oda domin ci gaban al'umma.
Zanga-zangar #EndBadGovernance ta riƙide zuwa tashin hankali a wasu ƙananan hukumomin jihar, wanda hakan ya ya kai ga asarar dukiyoyi.
Gwamnatin Kano ta cire dokar hana fita
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sanar da janye dokar hana fita da ta sanya.
A cikin wata sanawar da da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Halilu Baba Dantiye ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne biyo bayan gamsuwa da yadda al'amuran tsaro suka inganta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng