Dattawan Arewa Sun Gargadi Tinubu Kan Batun Canza Tsarin Mulkin Najeriya

Dattawan Arewa Sun Gargadi Tinubu Kan Batun Canza Tsarin Mulkin Najeriya

  • Masana sun tura sakon gargadi ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan canza tsarin mulkin Najeriya da aka nemi ya yi
  • Alhaji Tanko Yakasai da Farfesa Auwalu Yadudu sun bukaci shugaba Bola Tinubu ya yi taka-tsan-tsan kan maganar canza tsarin mulkin
  • Hakan na zuwa ne bayan kungiyar masu kishin kasa sun bukaci shugaban kasar ya canza tsarin mulkin a ziyarar da suka kai masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan siyasa da masana na cigaba da gargaɗin Bola Ahmed Tinubu kan maganar canza tsarin mulkin Najeriya.

Alhaji Tanko Yakasai da Farfesa Auwalu Yadudu sun bukaci shugaban kasar da ya sake tunani kan shawarin da aka ba shi.

Kara karanta wannan

Yadda yan adawa da kungiyoyi suka yi rubdugu ga Tinubu, aka yi batun tsige shi

Shugaba Tinubu
An gargadi Tinubu kan canza tsarin mulki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Auwal Yadudu ya yi gargaɗin cewa matsalar Najeriya ba tsarin mulki ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargaɗin Tanko Yakasai ga Tinubu

Alhaji Tanko Yakasai ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya guji yin gaggawa kan batun canza tsarin mulkin Najeriya.

Tanko Yakasai ya ce canza tsarin mulkin kasa abu ne da ya kamata a tattauna a kansa sosai domin kaucewa fadawa kuskure.

Haka zalika ya ce idan aka yi garaje kan lamarin za a iya shiga matsala da za ta iya haifar da babban rikici a faɗin Najeriya.

Tsarin mulki: Yadudu ya gargadi Tinubu

Masanin harkokin Shari'a, Farfesa Auwalu Yadudu ya nemi Bola Tinubu ya yi taka tsantsan kan batun canza tsarin mulkin Najeriya.

Farfesa Yadudu ya ce duk wani canji da za a yi kuma dole a tabbatar ya bi doka da tsari idan ana so ya zama tabbatacce.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

Haka zalika Yadudu ya ce a halin yanzu babbar matsalar Najeriya ba canza tsarin mulkin ba ce, ya ce matsalar ita ce amfani da tsarin mulkin yadda ya dace.

Bola Tinubu aikawa gwamnoni kudi

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya yi maganar makudan kudin da ya ce ya tura wa gwamnonin jihohi domin rage radadin tsadar rayuwa

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa daga bankin duniya kudin suka zo kuma ya fadi abubuwan da ya kamata gwamnoni su yi da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng