Gwamna Abba Ya Dauki Mataki Kan Dokar Hana Fita da Ya Sa a Kano
- Gwamnatin Kano ta ƙara sassautawa al'ummar jihar kan dokar hana fita da ta sanya sakamakon zanga-zangar da aka yi
- Gwamnatin ta janye dokar hana fitan gaba ɗaya bayan ta gamsu da yadda al'amuran tsaro suka inganta a jihar Kano
- Abba Yusuf ya miƙa godiyarsa ga jami'an tsaro, malamai da al'umma bisa haɗin kan da suka ba da yayin da aka sanya dokar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da janye dokar hana fita da ta sanya a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Halilu Baba Dantiye ne ya bayyana hakan.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kwamishinan ya sanar da hakan ne cikin wani saƙon faifan murya da ya aika mata da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Abba ya janye dokar?
Halilu Baba Dantiye ya bayyana cewa gwamnatin ta janye dokar ne bayan ta gamsu da yadda al'amuran tsaro suka inganta a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa godiyarsa ga jami'an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ganin zaman lafiya ya dawo a jihar.
Gwamnan ya kuma miƙa godiyarsa ga malamai bisa addu'o'in da suka riƙa yi, sannan ya godewa al'ummar jihar bisa haƙurin da suka yi a lokacin dokar hana fitan.
"Gwamnati bayan ta duba lamarin tare da samun gamsuwar cewa matsalar tsaro ta inganta sosai yanzu ta cire dokar hana fita gaba ɗaya. Yanzu mutane za su iya gudanar da harkokinsu cikin lumana bisa doka da oda."
"Gwamnan ya ƙara rokon a ci gaba da yin addu'a ga ƙasarmu, jiharmu domin samun zaman lafiya da ci gaba."
- Halilu Baba Dantiye
An yi hargitsi a Kano sakamakon zanga-zanga
An dai sanya dokar hana fitan ta tsawon sa'o'i 24 bayan an samu tashin hankali sakamakon kutsen da wasu suka yi a zanga-zangar nuna adawa da ƙuncin rayuwa.
Sai dai bayan kwana biyu an sassauta dokar daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana sannan daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Gwamnatin Katsina ta sassauta dokar hana fita
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta sake sauƙaƙa dokar hana fita da ta sanya a faɗin jihar sakamakon zanga-zanga.
Dokar ta hana zirga-zirga daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa karfe 7:00 na safe yanzu an mayar da ita daga ƙarfe 10:00 na dare zuwa ƙarfe 5:00 na safe a faɗin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng