Yadda Yan Adawa da Kungiyoyi Suka yi Rubdugu ga Tinubu, Aka yi Batun Tsige Shi

Yadda Yan Adawa da Kungiyoyi Suka yi Rubdugu ga Tinubu, Aka yi Batun Tsige Shi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cigaba da shan suka daga bangarori daban daban na Najeriya kan tsare tsaren gwamnatinsa
  • Kungiyoyin kwadago da manyan yan siyasa daga Kudu da Arewacin Najeriya na cigaba da sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku manyan kungiyoyi da yan siyasa da suka yi rubdugu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu na cigaba da shan suka bayan kammala zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

Hakan ya faru ne musamman wajen ganin an gama zanga zangar ba tare da kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar ba.

Kara karanta wannan

An yaba da jawabin Tinubu, an nemi ya cafke dan takarar shugaban kasa kan tutar Rasha

Bola Tinubu
Yadda Tinubu ya sha suka kan zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta yi rahoto kan yadda manyan yan siyasa biyu da kungiyoyin kwadago suka soki shugaban kasar kan yadda Najeriya ke cigaba da tafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan kwadago sun caccaki Tinubu

Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun yi zazzafan suka ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan yadda lamura ke tafiya a Najeriya.

Kungiyar kwadago ta ce tun farkon mulkin Tinubu ake musu barazana da sauran yan Najeriya wanda ta kira shugaban kasa kan daukar matakin gaggawa.

Obi ya bukaci Tinubu ya yi aiki tukuru

Peter Obi ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kawo ƙarshen matsalolin da suka haddasa zanga zanga a fadin Najeriya.

Obi ya ce akwai talauci sosai a Najeriya kuma wajibi ne ga gwamnati ta tunkari matsalar maimakon noke-noke.

Lukman ya yi maganar tsige Tinubu

Tsohon shugaba a APC, Salihu Lukman ya ce zanga zangar tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya kawai ta kai a tsige shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

Lukman ya fadi haka ne kasancewar matasan Najeriya sun ba gwamnatin tarayya lokaci amma ta gagara daukan mataki har aka yi zanga zangar.

N573bn: Tinubu ya tura sako ga gwamnoni

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi maganar makudan kudin da ya ce ya tura wa gwamnonin jihohi domin rage radadin tsadar rayuwa.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa daga bankin duniya kudin suka zo kuma ta fadi abubuwan da ya kamata ayi da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng