Ministar Tinubu Ta Fadi Asarar da Tattalin Arziki Ya Samu Sakamakon Zanga Zanga

Ministar Tinubu Ta Fadi Asarar da Tattalin Arziki Ya Samu Sakamakon Zanga Zanga

  • Dr. Doris Uzoka Anite ta nuna takaicinta kan ta'annatin da aka yi wa tattalin arziƙi sakamakon zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci
  • Ministar ta masana'antu, ciniki da zuba jari ta bayyana cewa ɓarnar da aka yiwa tattalin arziƙin ta kai ta N500bn a dalilin zanga-zangar
  • Doris Anite ta kuma yi alhini kan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar wacce aka fara a ranar, 1 ga watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministar masana'antu, ciniki da zuba jari, Dr. Doris Uzoka Anite ta koka kan asarar da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndBadGovernance.

Ministar ta bayyana cewa ɓarnar da aka yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan sakamakon zanga-zangar ta kai ta N500bn.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

Doris Anite ta koka kan barna saboda zanga-zanga
Doris Anite ta ce an yi asarar N500bn sakamakon zanga-zanga Hoto: @DrDorisAnite
Asali: Twitter

Minista ta koka kan ɓarnar da aka yi

Doris Anite ta bayyana hakan ne a wani rubutu da ta yi a shafinta na X kan zangar-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar ta koka kan asarar rayukan da aka samu da kuma ɓarnar da aka yiwa ƴan kasuwa yayin zanga-zangar.

A cewarta, an lalata kayayyaki na kusan N52bn, yayin da adadin waɗanda suka mutu a zanga-zangar ya kai mutum 21.

"An mayar da tattalin arziƙi baya" - Minista

Ta bayyana cewa satar dukiyar jama’a sakamakon zanga-zangar wani koma baya ne ga harkokin kasuwanci da ƴan kasuwa a faɗin ƙasar nan.

"Abin baƙin ciki ne asarar rayukan da aka samu a lokacin zanga-zanga. Ina nuna alhini na ga iyalan waɗanɗa lamarin ya ritsa da su."
"Satar da aka yi wacce ta jawo asarar biliyoyi, koma baya ce ga tattalin arziƙinmu da ƴan kasuwa. Mu mutunta mutanen da muka rasa ta hanyar neman ƙarin kwanciyar hankali da tattaunawa mai ma'ana."

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

- Dr. Doris Uzoka Anite

Shettima ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana irin gata da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga matasan Najeriya.

Kashim wanda yake martani kan zanga-zanga ya ce Shugaba Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da taimakon matasa ta kowace hanya domin cigabansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng