Malamin Addini Ya Fadi Dalilin Kasa Magance Cin Hanci, Ya Kawo Mafita a a Najeriya

Malamin Addini Ya Fadi Dalilin Kasa Magance Cin Hanci, Ya Kawo Mafita a a Najeriya

  • Babban shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya koka kan yadda cin hanci da rashawa ke ci gaba da zama ruwan dare a ƙasar nan
  • Fasto Adeboye ya ce an kasa kawo ƙarshen matsalar ne saboda Kiristoci da ya kama su zama na daban sun koma suna karɓarsa
  • Ya buƙaci Kiristoci da su komar hanyar ubangiji sannan su guji karɓar cin hanci komai rintsin da za su tsinci kansu a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Babban shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya buƙaci Kiristoci su guji cin hanci da rashawa.

Fasto Adeboye ya bayyana haka ne a ranar Asabar lokacin taron shekara-shekara na cocin wanda aka gudanar a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Shekarau ya fadi dalilinsa na kin tsoma baki a rikicin masarautar Kano

Fasto Adeboye ya yi magana kan cin hanci
Fasto Enoch Adeboye ya yi magana kan cin hanci a Najeriya Hoto: Pastor E.A Adeboye
Asali: Facebook

Meyasa cin hanci ya yi ƙamari a Najeriya

Ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa ya ta'azzara a Najeriya ne saboda galibin kiristoci da ya kamata su zama na musamman da kuma kawo canji suna karɓarsa, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeboye ya bayyana cewa da tuni cin hanci da rashawa ya zama tarihi a ƙasar idan har kiristoci suka yanke shawarar za su daina karɓarsa komai rintsi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Muna maganar cin hanci da rashawa a Najeriya. Meyasa kuke ganin ya yi yawa sosai? Saboda mu Kiristoci, da ya kamata mu zama na musamman, ba mu kawo gyara ba. Yana da wuya a gane mutumin ƙwarai yanzu."
"Dole ne ka tsarkake kanka. Dole a ce mutane da sun hango ka za su san cewa wannan ya shirya zuwa Aljannah. A halayya da ɗabi'a dole ne ka bambanta."

Kara karanta wannan

Kaico: Ƴan bindiga sun hallaka basarake, sun yi awon gaba da mata da ƙananan yara

"Idan ana son ka ba da cin hanci saboda samun ƙarin girma, ka ƙyale musu abin su saboda kai mutum ne na musamman."
"Duniya za ta tsaneka saboda hanyar da ka bi wacce ita ce hanyar ubangiji."

- Fasto Enoch Adeboye

Fasto Adeboye ya caccaki mata masu kwalliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya caccaki matan da suke yin kwalliya kafin biki da kuma lokacin bukukuwan aurensu.

Fasto Adeboye ya ce irin wadannan matan wawaye ne kuma sun nuna cewa za su yi gyara ga yadda ubangiji ya tsara halittarsu tun kafin aurensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng