Shekarau Ya Fadi Dalilinsa Na Kin Tsoma Baki a Rikicin Masarautar Kano

Shekarau Ya Fadi Dalilinsa Na Kin Tsoma Baki a Rikicin Masarautar Kano

  • Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa yana ci masa tuwo a ƙwarya
  • Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa ya ƙi tsoma bakinsa a cikin rikicin ne saboda maganar tana gaban kotu
  • Shekarau ya yi fatan cewa za a warware rikicin nan ba da jimawa ba domin samun kwanciyar hankali a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan rikicin masarautar Kano.

Shekarau ya bayyana cewa rikicin na masarautar Kano ya dame shi, amma ba ya son tsoma bakinsa a ciki.

Shekarau ya yi magana kan rikicin masarautar Kano
Shekarau ya ce ba ya son yin magana kan rikicin masarautar Kano Hoto: Malam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun yi garkuwa da babban malamin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Shekarau ya ce kan rikicin sarautar Kano?

Tsohon gwamnan ya ɗora laifin rikicin a kan ƴan siyasa, inda ya yi fatan cewa za a warware shi nan ba da jimawa ba.

"Ni babban mamba ne a majalisar masarautar kuma baya ga haka na yi mulkin jihar. Domin haka ni babban ɗan jihar ne."
A ranar da maganar ta kai kotu, na ce ba zan yi magana ba ko tsoma baki a cikinta ba duk abin da zai faru."
"Abin na damu na. Ni ɗan Kano ne. Ina son komai na Kano ya kasance cikin kwanciyar hankali. Muna nan muna jira sannan addu'a ta ita ce a kawo ƙarshen rikicin nan ba da jimawa ba."
"Za a samu kwanciyar hankali, muna buƙatar masarautun gargajiya. Ba zan yi magana sosai a kan hakan ba saboda ina ɗaya cikin masu riƙe da sarauta."

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

"Batun siyasa ne ya sanya muka tsinci kanmu cikin wannan rikicin. Idan da a ce ƴan siyasa ba su shiga ciki ba, sannan da an tuntuɓi masarautun gargajiyar, da ba mu samu wata matsala ba."

- Malam Ibrahim Shekarau

Shekarau ya aika saƙo ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya kamata gwamnatin Bola Tinubu ta sake duba manufofinta kuma ta amince da kura-kuranta.

Malam Shekarau ya ce lokaci da ya yi da Tinubu da muƙarrabansa za su sake nazari kan tsare-tsaren da suka jefa ƴan Najeriya cikin wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng