Yan Bindiga Sun Kai Harin 'Bom' Kan Jami'an Tsaro, An Yi Asarar Rai a Najeriya

Yan Bindiga Sun Kai Harin 'Bom' Kan Jami'an Tsaro, An Yi Asarar Rai a Najeriya

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari kan ƴan sanda a shingen binciken ababen hawa a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas
  • Rundunar ƴan sanda ta ce maharan sun yi amfani da bom suka kashe ɗan sanda ɗaya a harin tare da jikkata wani mutum ɗaya
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Ikenga ya ce tuni aka fara farautar maharan domin doka a yi aiki a kansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda a wani kazamin hari da suka kai shingen bincike a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya. 

Lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a a wani shingen binciken ‘yan sanda da ke kauyen Uruagu a karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Kara karanta wannan

Kaico: Ƴan bindiga sun hallaka basarake, sun yi awon gaba da mata da ƙananan yara

Sufetan yan sandan Najeriya.
Dan sanda ya mutu a harin bam da ƴan bindiga suka kai a kudancin Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yan sanda sun tabbatar da lamarin

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da kai harin da kuma kisan jami'inta guda ɗaya, kamar yadda Premium Times ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Jumu'a, kakakin ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya ce da farko maharan sun bude wuta amma ƴan sanda suka fatattake su.

SP Ikenga ya ƙara da cewa bayan haka ne ƴan bindigar suka jefawa jami'an ƴan sanda bom, wanda ya tarwatse a wurin.

Ƴan bindiga sun tashi bom

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce tashin bom ya hallaka ɗan sanda ɗaya yayi da wani kuma ya ji munanan raunuka a lokacin artabu da maharan.

A cewarsa, yanzu haka ɗan sandan ya samu raunuka a harin yana kwace a asibiti ana kula da lafiyarsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane sama da '30' a Arewa

Mista Ikenga ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar Anambra, Nnaghe Obono, ya bayar da umarnin farautar waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

"Tuni tawagar farautar makasan karkashin mataimakin kwamishinan ƴan sanda na Nnewi ta fara aiki da mazauna yankin domin bankaɗo ƴan bindigar da cafke su," in ji shi.

Masu garkuwa sun nemi fansa a Kogi

Rahoto ya zo cewa Masu garkuwa da ɗaliban jami'ar jihar Kogi (KSUK) sun turo sakon kuɗin fansar da suke bukatar a biya kafin su sake su.

Maharan sun sace ɗaliban jami'ar su biyu tare da kantoman karamar hukumar Kabba/Bunu da hadimansa ranar Jumu'a, 2 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262