Olusegun Obasanjo Ya Bayyana Hanyar da Najeriya Za Ta Samu Ci Gaba

Olusegun Obasanjo Ya Bayyana Hanyar da Najeriya Za Ta Samu Ci Gaba

  • Olusegun Obasanjo ya yi magana kan batun ƙasar nan ta koma amfani da wa'adin mulki ɗaya na shekara shida
  • Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa hakan ba shi ne abin da ƙasar nan ke buƙata ba domin samun ci gaban da ake buƙata a ƙasar nan
  • Obasanjo ya yi nuni da cewa ƙasar nan za ta samu ci gaba ne kawai idan shugabanni da ƴan ƙasa sun sauya tunaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan batun kawo tsarin wa'adin mulki ɗaya na shekara shida.

Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya ba za ta samu ci gaban da take buƙata ba har sai shugabanni da al'ummarta sun sauya ɗabi'unsu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana dalilin kasa cafke 'yan bindigan da ke nuna kansu a duniya

Obasanjo ya yi magana kan shugabanci a Najeriya
Obasanjo ya fadi matsalar Najeriya Hoto: Leigh Vogel
Asali: Getty Images

Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu ƴan majalisar wakilai shida a birnin Abeokuta ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya yi gargaɗi

Tsohon shugaban ƙasan ya yi gargaɗin cewa akwai matsala babba da za ta biyo baya idan har shugabanni suka kasa ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalolin ƙasar nan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Idan aka ba wani wa'adin mulki ɗaya na shekara shida, za su iya yin cutar da za su yi a cikin wa'adin mulki biyu na shekara huɗu. Bambancin kawai shi ne za su iya a cikin shekara shida maimakon shekara huɗu."
"A wajena wannan ba shi ne matsalarmu ba. Mu ne matsalar kanmu, sannan idan ba mu kula da kanmu ba, ko da mun koma amfani da wa'adin mulkin shekara shida ko na shekara huɗu, babu abin da zai sauya indai har ba mu sauya tunani kan yadda muke gudanar da abubuwa ba."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya aike da saƙon gaggawa ga Tinubu kan masu zanga zanga

"Saboda haka matakin farko ya fara ne daga kanmu. Eh dole mu sake tunani kan dimokuraɗiyyarmu, amma halin mutanen da ke cikin gwamnati dole ne ya sauya."
"Tare da dukkan girmamawa, kamata ya yi a ce da yawa daga cikin mutanen da ke cikin gwamnati a halin yanzu suna ɗaure a gidan yari."

- Olusegun Obasanjo

Karanta wasu labaran kan Obasanjo

Obasanjo ya gargaɗi shugabanni

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi shugabanni da sauran ƴan Najeriya a kan su rungumi sulhu domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Obasanjo ya bayyana cewa nauyi ne babba ya rataya a wuyan shugabanni na yin adalci da samar da cigaba mai dorewa domin wanzuwar zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng