Daga Karshe 'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Kai Samame a Hedkwatar Kungiyar NLC

Daga Karshe 'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Kai Samame a Hedkwatar Kungiyar NLC

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fito ta yi magana kan dalilinta na kai samame a hedkwatar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC)
  • Rundunar ta musanta cewa samame ta kai, inda ta ce ta bi sahun wani ɗan ƙasar waje ne da ake zargi da aikata laifuka
  • NLC dai ta yi zargin cewa jami'an ƴan sanda da na hukumar DSS sun kai samame a hedkwatarta cikin dare inda suka kwashi takardu da wasu abubuwa masu muhimmanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun bi sahun wani wanda ake zargi zuwa wani shago a ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC).

Ƙungiyar ta NLC dai ta zargi jami’an ƴan sanda da na hukumar DSS da kai wa ofishinta na Abuja samame a daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

NLC ta yi martani mai zafi bayan jami'an tsaro sun kai samame a hedkwatarta

'Yan sanda sun kai samame hedkwatar NLC
'Yan sanda sun je neman mai laifi a hedkwatar NLC Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Dalilin ƴan sanda na zuwa hedkwatar NLC

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a shafin X, kakakin rundunar ƴan sandan, Muyiwa Adejobi, ya yi ƙarin haske kan dalilin zuwansu hedkwatar ƙungiyar NLC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne domin cafke wani ɗan kasar waje da ke da hannu wajen aikata laifuka da dama a faɗin Najeriya da sauran ƙasashen Afirika.

"Rundunar ƴan sandan Najeriya ta lura da wasu rahotanni da ke zargin cewa ƴan sanda sun kai samame a sakatariyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC, wacce aka fi sani da Labour House, da ke tsakiyar babban birnin tarayya Abuja."
"Rundunar ƴan sandan Najeriya na son bayyana cewa an bi sahun wani wanda ake zargi a wani bincike da ake yi zuwa wani shago a cikin ginin cibiyar kasuwanci ta Abuja."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnatin Tinubu ta aika da muhimmin sako ga kasashen waje

"Jami'an tsaro ɗauke da makaman da suka dace sun gudanar da aiki a wajen, wanda ya kasance ginin ƙungiyar NLC.
"Wannan aikin wanda aka tsara bisa doka, an gudanar da shi ne domin cafke wani ɗan ƙasar waje wanda ake zargi da hannu a aikata laifuffuka da dama a Najeriya da ƙasashen Afirika."

- Muyiwa Adejobi

NLC ta magantu kan dakatar da zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta dakatar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.

Ƙungiyar NLC ta kuma musanta cewa ta sake matsayarta kan zanga-zangar wacce ake yi a faɗin ƙasar nan domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng