Zanga Zanga Na Lafawa, Dalar Amurka Ta Karye a Kasuwar Musayar Kudi a Najeriya
- Ƙimar Naira ta ƙaru kasuwar hada-hadar kuɗi ta bayan fage da farashin gwamnati ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2024
- Bayanai sun nuna darajar kuɗin Najeriya ya tashi zuwa N1,590 daga N1,595 da aka yi musaya kan kowace Dala ranar Laraba a kasuwar bayan fage
- Wannan na zuwa ne a lokacin da zanga-zanga kan yunwa ta fara lafawa a faɗin ƙasar nan kwanaki ƙalilan gabanin karewar wa'adin da aka ɗiba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yayin da zanga-zanga kan hauhawar farashi da yunwa ta fara lafawa a Najeriya, ƙimar kuɗin ƙasar ya ƙaru a ƙasuwar cinikayyar kuɗin ƙasashen ƙetare.
A jiya Alhamis, 8 ga watan Agusta, darajar Naira ta ƙaru, inda aka yi musaya a farashin N1,590 kan kowace Dala ɗaya daga N1,595/1$ na ranar Laraba a kasuwar bayan fage.
Naira ta tashi a farashin gwamnati
Haka nan kuma darajar Naira ta tashi zuwa N1,596.52 a farashin kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ta Najeriya (NAFEM), rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa farashin canji na NAFEM ya sauka zuwa N1,593.62 kan kowace Dala daga N1,596.52/1$ na ranar Laraba.
Hakan na nufin darajar Naira ta ƙaru da N2.9 a farashin gwamnati ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta idan aka kwatanta a farashin da aka yi canji ranar Laraba.
Hada-hadar canjin Dala ta ƙaru
Adadin Dalar Amaurka da aka yi ciniki a kasuwa ya karu da kashi 51% zuwa $141.99m daga $93.92m da aka yi hada-hada da su a ranar Laraba.
Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin fashin kasuwar ƴan canji da farashin NAFEM na gwamnati ya karu zuwa N3.52 kan kowace Dala daga N1.52/$1 a ranar Laraba.
Gwamna Bala ya soki Tinubu
A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ɗora laifin halin ƙuncin rayuwar da ake ciki kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Sanata Bala Mohammed ya ce tsare-taren tattalin arziƙi na gwamnatin APC ne ya kawo ƙunci, yunwa da wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng