Zanga Zanga: Gwamnan Plateau Ya Dauki Matakin Saukakawa Jama'a

Zanga Zanga: Gwamnan Plateau Ya Dauki Matakin Saukakawa Jama'a

  • Gwamnatin jihar Plateau ta sassauta dojar hana fita da ta sanya a birnin Jos da Bukuru sakamakon zanga-zangar da ake yi
  • Gwamna ya sassauta dokar, an ba jama'a damar fitowa su gudanar da harkokinsu daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa ƙarfe 6:00 na yamma
  • Caleb Mutfwang ya yabawa jama'a bisa haɗin kan da suka bayar inda ya buƙace su da su ci gaba da ba hukumomin tsaro haɗin kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta ƙara sassauta dokar hana fita da ta sanya a birnin Jos da Bukuru na jihar.

A yanzu gwamnati ta ba mutane damar yin zirga-zirga cikin walwala daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa karfe 6:00 na yamma a kullum.

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

Gwamnan Plateau ya sassauta dokar hana fita
Gwamnati ta sassauta dokar hana fita a Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Twitter

Gwamnatin Plateau ta sassauta doka

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan jihar, Gyang Bere, ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gyang Bere ya bayyana cewa an sassauta dokar hana fitan ne daga ranar Alhamis bayan da Gwamna Caleb Mutfwang ya tattauna da hukumomin tsaro tare da yin duba kan yanayin tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

Gwamna Mutfwang ya yabawa jama'a

The Punch ta ce Gwamna Mutfwang ya yabawa jama’a bisa yadda suka kwantar da hankulansu a lokacin dokar hana fitan, sannan ya buƙaci su ci gaba da bayar da haɗin kai ga hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

"Duba da samun yanayin tsaro mai kyau a Jos da Bukuru, gwamnatin jihar Plateau ta sake sassauta dokar hana fita wacce za ta fara aiki daga yau Alhamis, 8 ga watan Agustan 2024."

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

"An ba jama'a iznin yin zirga-zirga domin gudanar da harkokinsu daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa ƙarfe 6:00 na yamma har zuwa lokacin da za a sake bayar da sanarwa."

- Gyang Bere

Mutane sun samu sauƙi

Maryam Isma'il ta bayyanawa Legit Hausa cewa tabbas jama'a za su sauki sakamakon sassauta dokar da aka yi.

Ta bayyana cewa an girke jami'an tsaro domin tabbatar da cewa mutane sun bi dokar sau da ƙafa.

"Eh tabbas za a samu sauƙi wajen gudanar da harkokin yau da kullum kuma matakin abin a yaba ne. Sai dai matsalar da muka fuskanta ita ce ƴan kasuwa sun ƙarawa kayayyakinsu farashi."

- Maryam Isma'il

Gwamna Uba Sani ya sassauta dokar kulle

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Malam Uba Sani ya tausayawa mutane, ya sassauta dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka sanya a birnin Kaduna da Zaria.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi darasin da ya kamata gwamnonin Arewa su dauka kan zanga zanga

Gwamnan ya sassauta dokar, inda ya ba al'umma damar fita su gudanar da harkokinsu na yau da kullum daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng