Matasa Sun Fusata da Kashe Ɗan Uwansu, Sun Bankawa Fadar Basarake Wuta a Arewa
- Matasa sun ƙona fadar Hakimin Lere da ke ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa a jihar Bauchi bayan kisan ɗan uwansu matashi
- Mazauna yankin sun bayyana cewa matasan sun huce fushinsu kan hakimin ne bisa zargin shi ya ƙarfafawa sojoji guiwa su sanya dokar hana fita
- Rahotanni sun nuna an yi hatsaniya tsakanin sojoji da wasu ƴaƴan PDP a garin Lere, lamarin da ya zama ajalin mutum ɗaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi -Wasu fusatattun matasa a sun kona fadar Hakimin Lere da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun bankawa fadar wuta ne sakamakon rikicin da ya faru tsakanin sojoji da magoya bayan jam'iyyar PDP na garin Lere.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sojojin sun kashe mutum ɗaya, Habibu Aminu yayin da wasu mutane shida kuma suka samu raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta hannun mai magana da yawunta, SP Ahmed Wakili.
Meyasa matasa suka ƙona fadar hakimin?
Wani mazaunin Lere da aka harba a ido lokacin da sojojin suka kai samame, Zaharedden Mohammed, ya ce matasa sun ƙona fadar ne kan zargin da suke wa hakimi.
A cewarsa, fusatattun matasan sun taɓa fadar basaraken bisa zargin shi ya sa sojoji su sanya dokar zaman gida a yankin, rahoton Daily Post.
"Wasu daga cikin matasan tawagar kamfen PDP suna takun saƙa da sojoji, wannan ya sa sojojin suka fake da dokar hana fita domin su farmaki wasu mutane."
Yadda aka ƙona fadar hakimin Lere
Wani mutumin garin Lere, Alhaji Sule Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa matasan sun huce haushin su ne a kan fadar hakimi.
"A ranar Laraba, fusatattun matasan suka je fadar basaraken kuma suka banka mata wuta,"
- Mazaunin garin Lere
Duk wani ƙokarin jin ta bakin Hakimin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
DSS ta kai samame hedkwatar NLC
A wani labarin kun ji cewa jami'an tsaro sun kai samame hedkwatar kungiyar kwadago ta kasa NLC a daren ranar Laraba kan zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan.
Masu gadin wurin sun bayyana cewa jami'an sun rufe fuskokinsu a lokacin da suka shiga wurin kuma kai tsaye suka nufi ofishin shugaban NLC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng