Ana Cikin Zanga Zanga, Shugaban NYSC Na Jiha Guda Ya Ɓata, Bayanai Sun Fito
- Jagoran hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) na jihar Akwa Ibom ya ɓata a kan hanyar zuwa wurin aiki
- Mai magana da yawun NYSC na kasa Eddy Megwa ya bayyana cewa ana zargin an yi garkuwa da shi ne a tsakanin Delta da Akwa Ibom
- Ya ce har yanzu babu wani labari game da inda ya shiga tare da direbansa, inda ya buƙaci duk wanda ke da wani bayani ya sanar da NYSC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta sanar da cewa kodinetanta na jihar Akwa Ibom, Mista Okun Christopher ya ɓata.
Hukumar ta bayyana ɓatan shugaban NYSC na jihar Akwa Ibom tare da direbansa Mista Daniel Effiong Asibong, kuma har yanzun ba a ji ɗuriyarsu ba.
Mai magana da yawun NYSC ta kasa, Eddy Megwa, ne ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Laraba a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NYSC na zargin an yi garkuwa da shi
Ya ce ana zargin an yi garkuwa da su ne a tsakanin jihohin Delta da Akwa Ibom a lokacin da suke hanyar zuwa wani aiki ranar Litinin, 29 ga Yuli, 2024.
Megwa ya koka da cewa tun daga lokacin da aka neme su aka rasa, duk wani kokarin gano inda suke bai cimma ruwa ba.
Ya ƙara da cewa a halin yanzun hukumar NYSC na ci gaba da tuntuɓar iyalansu domin samun masaniya kan ida suka shiga.
Wane mataki NYSC ta ɗauka?
Eddy Megwa ya roki duk wanda ya ke da muhimman bayanai kan inda suke da ya gaggauta zuwa ya sanar da NYSC.
"Duk wanda yake da sahihin bayani dangane da inda suke ya tuntubi ɗaya daga cikin sakatariyar NYSC da ke jihohi 36, ofisoshin yanki ko babbar hedikwata ta kasa da ke Abuja.
"Ko kuma ya kai rahoto caji ofis na ƴan sanda mafi kusa da shi ko kowane ofishin jami'an tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa," in ji shi.
Okun ya fara aikin a matsayin shugaban NYSC na 19 a jihar Akwa Ibom a watan Afrilun 2024, kamar yadda The Cable ta rahoto.
NYSC ta ɗage ayyukan watan Agusta
A wani rahoton kuma hukumar NYSC ta sanar da dakatar da dukkanin wasu ayyuka na masu yiwa kasa hidima na watan Agusta a fadin kasar nan.
An dage shirin tantancewa da hidimtawa al’umma na wata-wata (CDS) ga mambobin NYSC saboda zanga-zangar da ake yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng