Ana Cikin Zanga Zanga Tinubu Ya Aika Sako Mai Ratsa Zuciya Ga 'Yan Najeriya

Ana Cikin Zanga Zanga Tinubu Ya Aika Sako Mai Ratsa Zuciya Ga 'Yan Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya sake yin jawabi ga ƴan Najeriya yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara kai zuciya nesa kan halin matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta
  • Ya bayyana cewa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka za su farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan zuwa kan turbar da ta dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara kai zuciya nesa da gwamnatinsa.

Shugaban ƙasan ya ba da tabbacin cewa ƙasar nan tana samun tagomashi inda ta fara samun ci gaba maimakon koma bayan da ta samu a baya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

Tinubu ya roki 'yan Najeriya
Tinubu ya ba 'yan Najeriya hakuri Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Shugaba Bola Tinubu ya ba da haƙuri

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da fadar shugaban ƙasa ta sanya a shafinta na X a ranar Laraba, 7 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya amince cewa ana shan wuya a ƙasar nan sakamakon cire tallafin man fetur da sakin Naira sakaka.

Ya bayyana cewa wahalar da ƴan Najeriya ke sha ta haɗa ne da abin da ba za iya kauce masa ba na cire tallafin man fetur sannan da manufofinsa masu kyau ga ƙasar nan.

Me Tinubu ya ce ga ƴan Najeriya?

"Ƴan uwana ƴan Najeriya, wannan lokacin ya kasance mai wuya a garemu kuma ko tantama babu ya yi tsauri da yawa, amma ina roƙon ku da ku kawar da ido kan wuyar da ake sha ta ɗan lokaci, ku kalli abin da ke tafe nan gaba.

Kara karanta wannan

"Ba Tinubu ba ne": Jigo a PDP ya fadi mai laifi kan halin da Najeriya ke ciki

"Dukkanin kyawawan manufofinmu da ayyukanmu suna kan hanya. Abu mafi muhimmanci na san cewa za su haifar da ɗa mai ido."
"Ina roƙon ku da ku taimaka ku yarda cewa za mu iya kuma mun damu da jin daɗinku. Za mu fita daga wannan matsin. Sannan saboda matakan da muka ɗauka, Najeriya za ta ci moriyar gobenta mai kyau da ke jiranta."

- Bola Tinubu

Jawabin na Tinubu dai shi ke karo na biyu tun bayan da aka fara zanga-zanga sakamakon tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙasashen waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi barazanar ɗaukar mataki kan duk ƙasar da ke da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance da ake yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan masu kiran sojoji su kwace mulki, ya yi gargadi

Gargaɗin na gwamnatin tarayya na zuwa ne bayan wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa ɗaga tutocin ƙasashen waje, musamman na ƙasar Rasha.\

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng