Zanga Zanga: Gwamnatin Tinubu Ta Aika Muhimmin Sako Ga Kasashen Waje

Zanga Zanga: Gwamnatin Tinubu Ta Aika Muhimmin Sako Ga Kasashen Waje

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kaɗan ba za ta lamunce wasu ƙasashen waje su yi mata katsalandan a harkokinta na cikin gida ba
  • Ministan harkokin ƙasashen waje wanda ya bayyana hakan ya yi barazanar gwamnatim za ta ɗauki mataki kan duk ƙasar da ta samu da laifi
  • Kalaman ministan na zuwa ne bayan wasu ɗaga cikin masu zanga-zanga sun riƙa ɗaga tutocin ƙasashen waje suna kiran a kawo musu ɗauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi barazanar ɗaukar mataki kan duk ƙasar da ke da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance da ake yi a ƙasar nan.

Gargaɗin na gwamnatin tarayya na zuwa ne bayan wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa ɗaga tutocin ƙasashen waje, musamman na ƙasar Rasha.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun lakadawa masu zanga zanga duka a gaban 'yan sanda

Gwamnatin ta ja kunnen kasashen waje kan zanga-zanga
Gwamnatin tarayya ta gargadi kasashen waje kan zanga-zanga Hoto: @OfficialABAT, @YusufTuggar
Asali: Twitter

Wane gargaɗi gwamnatin Tinubu ta yi?

Ministan harkokin ƙasashen waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan tarayyar ya nanata cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ƴanci.

Sannan ba za a yarda ƴan ƙasashen waje masu ba da goyon baya ga masu zanga-zanga su yi katsalandan cikin harkokin cikin gida ba, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Matasa sun ɗaga tutocin Rasha

Matsayar gwamnatin ba ta rasa nasaba da yadda wasu masu zanga-zanga suke ɗaga tutocin ƙasar Rasha a wasu jihohin ƙasar nan.

Wasu daga cikinsu har kira suke yi ga shugaban ƙasa Vladimir Putin ya kawowa ƴan Najeriya ɗauki kan halin ƙunci da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan.

Sai dai, Rasha ta hannun ofishin jakadancinta da ke Abuja, ta nesanta kanta da masu zanga-zangar da ke ɗaga tutocinta tare da musanta cewa tana da hannu a wajen shirya zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya fadi manufar rikicin da aka samu sakamakon zanga zanga

Zanga-zangar wacce aka fara a ranar, 1 ga watan Agustan 2024, ta haifar da tashe-tashen hankula a wasu sassan ƙasar nan inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Rasha ta nesanta kanta da zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Rasha ta musanta cewa tana da hannu a ɗinkawa da ɗaga tutocin ƙasar da wasu masu zanga-zanga ke yi a Arewacin Najeriya.

Ofishin jakadancin Rasha a Najeriya wanda ya bayyana hakan, ya ce ko kaɗan ba su da hannu a tawagar matasan da aka ga suna ɗaga tutocin Rasha yayin da suka fito zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng