'Yan Daba Sun Lakadawa Masu Zanga Zanga Duka a gaban 'Yan Sanda

'Yan Daba Sun Lakadawa Masu Zanga Zanga Duka a gaban 'Yan Sanda

  • Wasu ƴan daba a jihar Rivers sun yi yunƙurin hana zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake yi a ƙasar nan a ranar Laraba
  • Ƴan daban sun yi dafifi a wurin da ake gudanar da zanga-zangar a birnin Port Harcourt inda suka yiwa mutum biyu duka
  • Ƴan daban ba su tsaya kan masu zanga-zanga kaɗai ba, inda suka ci zarafin wata ƴar jarida mai ƙoƙarin ɗaukar rahoto a wajen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wasu ƴan daba sun lakadawa wasu daga cikin masu zanga-zangar #EndBadGovernance duka a jihar Rivers.

Ƴan daban sun aikata hakan ne yayin da masu zanga-zangar suka taru domin ci gaba da nuna fushinsu kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnatin Tinubu ta aika da muhimmin sako ga kasashen waje

'Yan daba sun bugi masu zanga-zanga a Rivers
'Yan daba sun yiwa masu zanga-zanga duka a Rivers Hoto: : @PoliceNG/Benson Ibeabuchi
Asali: UGC

Ƴan daba sun bugi masu zanga-zanga

Tashar Channels tv ta ce ƴan daban sun kuma ci zarafin ma'aikaciyarta mai suna, Deborah Agbalam, a lokacin da take ƙoƙarin kawo rahotannin zanga-zangar a birnin Port Harcourt ranar Laraba. 

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gungun ƴan daban sun tsaya a kusa da sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Port Harcourt inda suke tsoratarwa tare da fatattakar masu zanga-zangar.

Shaidu sun bayyana cewa an lakaɗawa masu zanga-zanga mutum biyu duka yayin da jami’an ƴan sanda sama da 20 ke tsaye suna kallo ba su yi komai a kai ba.

Ƴan daba sun hana zanga-zanga

Ƴan daban sun bayyana cewa sun je ne domin tabbatar da cewa ba za a yi zanga-zanga a yau ba.

Sakatariyar gwamnatin tarayya dake kan titin Port Harcourt/Aba ta kasance wurin da masu zanga-zangar ke haɗuwa domin nuna adawa da halin matsin da ake ciki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun ƙara yin ɓarna, sun kai hari a sakatariyar jam'iyyar APC

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi kwamishinan ƴan sandan jihar Rivers Olatunji Disu, kan lamarin, ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru.

Olatunji Disu ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da bin diddigin lamarin da kuma hana sake aukuwar hakan nan gaba.

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

An shiga fargaba da masu zanga zanga suka tare tawagar motocin gwamna a Najeriya

Masu zanga zanga sun ƙara yin ɓarna, sun kai hari a sakatariyar jam'iyyar APC

Zanga zanga: Matasa sun kai hari gidan Sanatan APC, ya yi zazzafan martani

Masu zanga-zanga sun dira a gidan Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu zanga-zanga sun yiwa gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ƙawanya da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers.

Sai dai, masu zanga-zanga ba su samu damar shiga ciki ba saboda tarin jami'an tsaron da suka tarar a gidan na tsohon gwamnan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng