Tsohon Sanata Ya Fadi Manufar Rikicin da Aka Samu Sakamakon Zanga Zanga
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya yi Allah wadai da barnar da aka samu a sakamakon zanga-zanga da ake yi a faɗin ƙasar nan
- Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa rikicen-rikicen da aka samu a Arewacin Najeriya wani yunƙuri ne na kifar da gwamnati
- Ya yi zargin cewa an rabawa matasa kuɗaɗe da tutocin Rasha yayin zanga-zangar wacce ake yi domin nuna adawa da halin ƙuncin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan rikice-rikicen da aka samu sakamakon zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Sanata Shehu Sani, ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu a Arewacin Najeriya sakamakon zanga-zangar.
Wane zargi Shehu Sani ya yi?
Shehu Sani wanda aka yi hira da shi a tashar Channels tv ranar Talata, ya ce tashe-tashen hankulan wani yunƙuri ne na kifar da gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi zargin cewa kwana ɗaya kafin zanga-zangar an raba kuɗaɗe da tutocin ƙasashen waje a tsakanin matasa.
"Kwana ɗaya kafin zanga-zangar ƙarshe, an raba kuɗi ga matasa da tutocin ƙasar Rasha. Hakan ya nuna cewa gabaɗaya manufar zanga-zangar ba domin tsare-tsaren gwamnati ba ne."
"An yi yunƙurin samar da wani yanayi ne wanda za a kifar da gwamnati. Idan aka samu irin haka, za ka ga cewa akwai wanda ke kitsa yadda za a samu karya doka da oda."
- Shehu Sani
An yi rikici yayin zanga-zanga a Arewa
A yayin zanga-zangar da aka yi a Kaduna, Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya, wasu matasa sun riƙa ɗaga tutocin Rasha yayin da suke kiran sojoji da su amshi mulki.
An fara zanga-zangar #EndBadGovernance ne a ranar, 1 ga watan Agusta kuma ana sa ran za a ɗauki tsawon kwanaki 10 ana yi.
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Babban hafsan tsaro ya fadi laifin masu daga tutar Rasha, ya gargadi 'yan zanga zanga
- Gwamnatin tarayya ta dauki kwakkwaran mataki kan masu daukar nauyin zanga zanga
- Zanga zanga: Kwankwaso ya bayyana wanda zai dauki alhakin barnar da aka yi a Kano
Shehu Sani ya magantu kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani, ya yi magana kan abubuwan da ke sanyawa zanga-zangar lumana ta rikiɗe ta koma tashin hankali.
Shehu Sani ya bayyana cewa idan jami'an tsaro ɗauke da makamai suka harbi masu zanga-zanaga, tana iya rikiɗewa ta koma tashin hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng