Akpabio: Shehu Sani Ya Fadi Hanyar da Za a Iya Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio: Shehu Sani Ya Fadi Hanyar da Za a Iya Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

  • An yi ta kiraye-kirayen ganin shugaban majalisar dattawa, ya yi murabus biyo bayan kalaman da ya yi kan zanga-zangar yunwa a ƙasar nan
  • Kalaman na Godswill Akpabio dai sun tunzura ƴan Najeriya inda suka yi ta Allah wadai da abin da shugaban majalisar ya faɗa kan zanga-zangar
  • Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi bayanin yadda za a iya tsige Akpabio daga shugabancin majalisar dattawa ta 10 cikin sauki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya mayar da martani kan kiran da ake yiwa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Kirayen-kirayen dai sun biyo bayan kalaman da Akpabio ya yi na cewa shi da wasu a cikin gwamnati za su ci gaba da cin abinci yayin da ƴan Najeriya ke zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

Shehu Sani ya fadi hanyar tsige Akpabio
Shehu Sani ya bayyana hanyar da za a iya tsige Akpabio Hoto: Nigerian Senate, Shehu Sani
Asali: Facebook

An caccaki shugaban majalisa, Godswill Akpabio

Shugaban majalisar dattawan ya yi wannan kalaman ne a wani taron da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) ta shirya a jihar Rivers a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martanin da ta mayar kan kalaman na Akpabio, ƙungiyar Amnesty International Nigeria, a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, ta caccaki shugaban na majalisr dattawa.

Har ila yau, a ranar farko ta zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziƙi a Najeriya, kalaman #AkpabioMustGo sun yi ta yawo a ko'ina a faɗin ƙasar a manhajar X.

Shehu Sani ya bayyana hanyar tsige Akpabio

Da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana hanyar da za a iya bi domin a tsige Akpabio.

Shehu Sani ya bayyana cewa tsige shugaban na majalisar dattawa na buƙatar haɗin kan Sanatoci.

Kara karanta wannan

Duk da katobarar da ya yi, Akpabio ya sake neman wata bukata wajen 'yan Najeriya

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 6 ga watan Agusta.

"Cire Akpabio zai iya yiwuwa ne kawai idan wani sanata ya tuntuɓi takwarorinsa sannan ya samu adadin da ake buƙata domin a fara shirin tsige shi. Idan shirin ya samu tangarɗa, za a iya dakatar da sanatan har zuwa zaɓe mai zuwa. Wannan shi ne kawai."

- Shehu Sani

Akpabio ya roƙi ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta buƙaci masu shirin gudanar da zanga-zanga su dakatar da shirye-shiryensu domin amfanin al’ummar Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan bayan wani zaman gaggawa da Sanatocin suka yi a Abuja ranar Laraba, 31 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng