Jam'iyyar APC Ta Dauki Sabon Mataki Kan Sanata Ali Ndume

Jam'iyyar APC Ta Dauki Sabon Mataki Kan Sanata Ali Ndume

  • Jam'iyyar APC ta zauna da sanata mao wakiltar Borno ta Tsakiya, Sanata Ali Ndume, bisa kalaman da ya yi a kan shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Ali Ndume ya ba da haƙuri kan kalaman da ya yi
  • Ganduje ya ƙara da cewa za su rubuta wasiƙa ga majalisar dattawa domin buƙatar ta sake duba matsayarta kan tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ya gayyaci Sanata Ali Ndume.

Kwamitin ya gayyaci Sanata Ali Ndume ne domin ya yi bayani kan kalamansa na baya-bayan da ya yi kan shugaban ƙasa Bola Tinubu waɗanda suka sanya aka tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

"Ba Tinubu ba ne": Jigo a PDP ya fadi mai laifi kan halin da Najeriya ke ciki

Jam'iyyar APC ta zauna da Ali Ndume
Sanata Ali Ndume ya ba jam'iyyar APC hakuri Hoto: Senator Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Ali Ndume ya ba APC haƙuri

Da yake magana bayan taron, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar ta gamsu da haƙurin da Ndume ya ba da, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na APC ya bayyana cewa za su sanar da majalisa hakan domin duba yiwuwar sauya matsayarta kan raba shi da muƙaminsa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Mun gamsu ƙwarai da haƙurin da ya ba da. Kamar yadda ya faɗa mun gayyace shi sannan kamar yadda kuka sani jam'iyya tana gaba da kowa."
"A matsayinmu na jam'iyya, za mu iya kiran ƴan majalisa, za mu iya kiran mambobin zartaswa, za mu iya kira duk ƴan jam'iyya waɗanda aka ba muƙami a gwamnati. Wannan shi yasa muka yanke shawarar mu zauna da shi."
"Matsala ce ta cikin gida da muke buƙatar mu warware sannan za mu rubuta takarda zuwa ga majalisa domin sanar da ita abin da ya faru tsakanin jam'iyya da Ali Ndume."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ba zai lamunta ba a Najeriya

"Kun san cewa ya ba jam'iyya haƙuri sannan za mu sanar da majalisa hakan tare da fatan cewa za ta sake yin duba kan matsayarta."

- Abdullahi Umar Ganduje

Sanata Ndume ya amsa kuskurensa

A na sa ɓangaren Sanata Ali Ndume ya amsa cewa maimakon ya fito ya yi ƙorafi a idon duniya, kamata ya yi a ce ya fara miƙa ƙorafinsa ta hannun shugabannin jam'iyyar.

Sanatan ya ƙara da cewa jam'iyyar ba ta kore shi ba, inda ya nuna cewa ko kaɗan ba shi da shirin ficewa daga APC.

Ndume ya ƙi karɓar sabon muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Ali Ndume, ya yi watsi da naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon buɗe ido.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya ba Ali Ndume sabon muƙamin biyo bayan tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar.

Kara karanta wannan

Ana jira ya dawo da tallafi, Tinubu ya aika da sako mai zafi ga masu zanga zanga

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng