Kano: An Kama Hatsabibin 'Barawon' da Ya Fitini Mutane da Fashi Zai Tsere Bayan Sace N15m

Kano: An Kama Hatsabibin 'Barawon' da Ya Fitini Mutane da Fashi Zai Tsere Bayan Sace N15m

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kano ta sanar da nasarar kama babban dan bindiga da ya fitini jihar da yawan sace sace
  • Kakakin yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya fitar da sanarwar tare da bayyana yadda jami'ansu suka samu nasarar cafke shi
  • Har Ila yau, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana yadda suka kama ɗan ta'addar da bindigogi da kuma tarin harsashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar yan sanda a Kano ta sanar da cafke wani barawo da ake zargin ya fitini al'ummar jihar.

Rahotanni sun nuna cewa an kama barawon ne bayan zargin ya sace miliyoyin kudi daga gidan wani mutum a ƙaramar hukumar Kunci.

Kara karanta wannan

"Mun tsaurara matakan tsaro," Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita

Kano Najeriya
Yan sanda sun kama babban barawo a Kano. Hoto: Legit
Asali: Original

Legit ta tatttaro bayanan da yan sanda suka yi ne a cikin wani sako da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama babban ɓarawo a jihar Kano

Rundunar yan sanda ta sanar da cewa ta samu korafi daga wani mutum a ƙaramar hukumar Kunci kan ɓarawo ya shiga gidansa ya sace kudi kimanin Naira miliyan 15.

Biyo bayan haka, kwamishinan yan sanda a jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya umurci jami'ansa da kokarin cafke ɓarawon cikin gaggawa.

Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da satar mai suna Hassan Iliya a karamar hukumar Musawa a jihar Katsina yana kokarin guduwa a kan babur wanda dama daga chan ya taho Kano.

Kano: Abubuwan da aka samu wajen ɓarawon

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kama abubuwa da yawa wajen Hassan Iliya ciki har da kudi N4.9m.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jami'an DSS sun kama masu ɗaukar nauyin telolin tutar Rasha a Kano

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa ta kama bindigogi kirar AK47 guda biyu da tarin harsashi a tattare da mutumin da ake zargin.

Kwamishinan yan sanda a jihar Kano ya yi kira ga al'umma kan saka ido da lura da duka wani motsin miyagun mutane a fadin jihar.

An kama wani barawo a garin Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke babban ɓarawo da ake zargin ya fitini al'umma da sace-sace.

Ɓarawon da ake zargi mai suna Glory Samuel ya sace makudan kudi da kayayyaki na miliyoyin kudi daga mutane da dama a jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng