"Ba za Mu Fasa ba," Kungiyar Matasa ta Dage kan Cigaba da Zanga Zanga

"Ba za Mu Fasa ba," Kungiyar Matasa ta Dage kan Cigaba da Zanga Zanga

  • Yayin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke neman jama'a su yi hakuri da batun zanga-zanga su hau teburin sulhu, kungiyar matasa ta ce ba fashi
  • Kungiyar Nigerian Patriotic Front Movement ta bayyana cewa za ta ci gaba da fitowa titunan Kano domin adawa da manufofin gwamnati
  • Sakataren kungiyar, Kwamred Anas Adamu da ya bayyana matakinsu ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin kasar nan ta gaza daukar mataki kan bukatunsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar Nigerian Patriotic Front Movement ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar Kano tun da gwamnati ta ki biya masu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Manyan 'yan siyasa da kungiya da suka kushe jawabin Tinubu

Sakataren kungiyar, Kwamred Anas Adamu ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa duk da shafe kwanaki ana zanga-zanga, shugaba Bola Tinubu bai dauki mataki ba.

Benson Ibeabuchi
Matasa za su ci gaba da zanga-zanga a Kano Hoto: Benson Ibeabuchi
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa dukkanin 'yan kasar nan na fuskantar matsalolin tattalin arziki da shugabanni watanni 15 bayan ya kama mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu gamsu da Tinubu ba" - 'Yan zanga-zanga

Matasan kasar nan sun bayyana cewa ba su gamsu da yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da salon mulkin kasar nan ba.

Sakataren kungiyar, Anas Adamu ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu bai dauki matakan kula da matsalolin talakawan Najeriya.

"Daya daga cikin bukatunmu ga gwamnatin Najeriya shi ne rage farashin man fetur zuwa yadda Tinubu ya same shi a kan N160-N200," inji Anas Adam

Sakataren ya kara da cewa su mutane ne masu bin doka da oda, shi ya sa su ka dakatar da zanga-zangar a Kano bayan sanya dokar hana zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Zanga zanga: An kama matashi a Kano

A baya mun ruwaito hukumomin tsaro a kasar nan sun cafke wani matashi da ake zargi da dinka tutar kasar Rasha tare da rabawa ga matasa a jihar Kano domin dagawa yayin zanga-zanga.

Tun bayan fara gudanar da zanga-zanga ne matasa su ka rika daga tutar Rasha, amma lamarin ya kara kamari a ranar Litinin dinnan har ya jawo hankalin mahukunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.