IPOB Ta Zargi Gwamnati da Goyon Bayan Nunawa Ibo Wariya, Ta Kawo Batun Ballewa daga Najeriya

IPOB Ta Zargi Gwamnati da Goyon Bayan Nunawa Ibo Wariya, Ta Kawo Batun Ballewa daga Najeriya

  • Kungiyar 'yan awaren kabilar Ibo ta nemi gwamnatin tarayya ta amince da a ba su damar kada kuri'a domin zabar makomarsu
  • Jami'in hulda da jama'a na haramtacciyar kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyana matsayarsu ta cikin wata sanarwa
  • Ya ce a shirye su ke su bar Najeriya ta halastacciyar hanya ba tare da neman tashin hankali ba tun da 'yan Kudu maso Yamma ba sa sonsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Haramtacciyar kungiyar 'yan awaren IPOB ta bukaci gwamnatin Najeriya ta ba ta damar kada kuri'a domin barin kasar nan.

Wannan bukata ta biyo bayan karuwa nuna kin jinin kabilar Ibo a wasu sassan Kudu maso Yammacin kasar nan.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da 'mummunan mulki': 'Yan Najeriya sun yi martani ga jawabin Tinubu

Kungiyar IPOB
IPOB ta nemi ficewa daga cikin Najeriya ta hanyar kada kuri'a Hoto: @therleez
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa kakakin haramtacciyar kungiyar, Emma Powerful ya caccaki gwamnatin Babajide Sanwo-Olu saboda barin jama'a su na nuna wariya ga 'yan kabilar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai barazana ga lafiyar kabilar Ibo," IPOB

Haramtacciyar kungiyar 'yan awaren kabilar Ibo ta IPOB ta bayyana damuwa kan kare rayuka da dukiyoyin 'yan kabilar a sassan Kudu maso Yammacin kasar nan.

Kungiya ta yi zargin wasu kusoshin gwamnatin Babajide Sanwo-Olu da ta Bola Tinubu da daukar nauyin masu nuna adawa da zaman 'yan kabilar Ibo a jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Emma Powerful, wanda shi ne kakakin kungiyar na ganin idan su ka fice daga cikin kasar ta ruwan sanyi, za a samu kyakkyawar alaka tsakaninta da Najeriya.

"IPOB ba za ta iya ba," Farfesa

Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a jami'ar Abuja, Farfesa Farouq BB Farouq ya shaidwa Legit cewa kurari kawai IPOB ke yi, inda ya ce hanyar neman shugabanci ce kawai.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: CUPP ta bayyana babban kuskuren da zai iya jefa Tinubu a matsala

Ya ce a baya lokacin da Awolowo ya nemi a ba wa kowa dama ya iya neman ficewa daga kasar a shekarar 1951-1958 da ake tsarin mulki, Ibo ne da hadin kan turawa da 'yan Arewa ne su ka ki amincewa da hakan.

Kotu ta yi watsi da karar shugaban IPOB

A baya mun kawo labarin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da karar da shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar gabanta.

Gwamnatin tarayya na shari'a da Nnamdi Kanu saboda zarginsa da cin amanar kasa ta hanyar kokarin tayar da hatsaniyar neman ballewa daga kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.