Bidiyo Ya Bazu, Jami'in Tsaro Ya Harbe Matashi Har Lahira Ana Tsaka da Zanga Zanga
- An shiga yanayin tashin hankali yayin da wani jami'in tsaro ya harbe mai zanga-zanga har lahira a garin Azare da ke jihar Bauchi
- Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wasu mutane suna tarar wa matashin suna dukansa, daga karshe jami'an tsaron ya harbe shi
- Hakan na zuwa ne bayan an yi arangama.tsakanin masu zanga zanga a jami'an ƴan sanda a gaban sakataruyat karamar hukumar Katagum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - An ɗauki bidiyon wani jami'in tsaro a lokacin da ya sa bindiga ya harbe mai zanga-zanga har lahira a Azare, ƙaramar hukumar Katagum da ke Bauchi ranar Litinin.
Faifan bidiyon ya nuna yadda wasu mutane biyu suka azabtar da matashin, ɗaya daga cikin masu zanga-zanga wanda ba a gano bayanansa ba har yanzu.
Jaridar Daily Trust ta ce matashin na kwance a ƙasa yayin da wasu mutum biyu zuwa uku suka kewaye shi suna ta bugunsa babu ƙaƙƙautawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe mai zanga-zanga
Jim kaɗan bayan haka ne makashin, wanda ake zargin jami'an tsaro ne ya matsa kusa da wurin da ake bugun matashin.
Bayan ya buge shi har sau biyu, sai jami’in tsaron ya saita shi da bindiga, ya danna kunama nan take ya harbe shi har lahira.
Mutanen da ke wurin sun yi ihu a lokacin da jami'in ɗan sandan ya gudu ba tare da ya waiwayo ba.
Menene gaskiyar bidiyon?
A wani binciken kwakwaf da aka gudanar kan lamarin, an gano cewa faifan bidiyon na gaskiya ne ba haɗa shi aka yi ba.
Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a gaban sakatariyar karamar hukumar Katagum, inda ‘yan sanda da wasu masu zanga-zanga ɗauke da tutar Rasha suka yi arangama.
Wani mazaunin garin Azare da bai so a ambaci sunansa ya bayyana cewa matashi na daya daga cikin ‘yan iskan da ‘yan sanda suka kama, rahoton Channels tv.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, bai bada amsar sakon da aka aika masa kan lamarin ba.
An kama mai ɗinka tutar Rasha
Kuna da labarin jami'an tsaro sun kama wani tela mai suna Ahmed bisa zarginsa da yaɗa tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano a lokacin zanga-zanga
Rahotanni sun nuna matasa sun fara ɗaga tutocin ƙasar ketaren ne a makon da ya wuce, amma lamarin ya ƙara ƙamari a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng