Tsadar Rayuwa: Zanga Zanga Ta Birkice, Matasa Sun Toshe Hanyoyi
- Matasan Najeriya na cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya da aka fara tun ranar 1 ga watan Agusta
- Wasu masu zanga zanga a jihar Osun da ke kudancin Najeriya sun fice daga wuraren da aka ware musu zuwa kan hanyoyin jihar
- Matasa masu zanga zanga sun bayyana muhimman abubuwan da suke buƙata shugaba Bola Tinubu ya musu da gaggawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Osun sun dauki sabon salo.
Rahotanni na nuni da cewa a yau Litinin matasan sun fice daga filin da hukuma ta ba su domin yin zanga zanga.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa fitar matasan daga filin ya jawo tsaiko ga al'umma da dama musamman matafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun toshe hanya a Osun
A safiyar yau aka ruwaito cewa matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Osun sun fice daga dandalin Mandela Freedom Park da aka tanada musu.
Vanguard ta wallafa cewa biyo bayan haka, matasan suka fito kan tituna a jihar inda suka kawo tsaiko ga ayyukan yau da kullum.
Osun: Jami'an tsaro sun bude hanyar
Bayan toshe hanyoyin, gamayyar jami'an tsaro da suke lura da masu zanga zangar suka kutsa tsakaninsu domin bude hanyoyi.
Jami'an tsaron sun hada da yan sanda, jami'an tsaro na farin kaya, jami'an shige da fice da jami'an kiyaye haɗura da sauransu.
Bukatun masu zanga zanga a Osun
Daya daga cikin masu zanga zangar mai suna Akin Ashafat ya ce za su cigaba da zanga zangar har sai an biya musu bukatunsu.
Masu zanga zangar sun bukaci Bola Tinubu ya dawo da tallafi man fetur da sauke farashin abinci maimakon ya rika kiransu zuwa tattaunawa.
Yan Najeriya sun yi martani ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya inda ya amince da koke-kokensu tare da bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa.
‘Yan Najeriya sun mayar da martani kan jawabin Tinubu a shafukan sada zumunta, inda wasu ke nuna goyon baya yayin da wasu ke sukarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng