Zanga Zanga: 'Yan Sanda Sun Jaddada Dokar Hana Fita a Katsina
- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta jaddada dokar hana zirga-zirga inda ta ja kunnen wadanda ke shirin fita zanga-zanga
- A wasu wuraren da ke jihar, an sanya dokar hana fita na awanni 24, inda a wasu wuraren aka sanya ta awa 12
- Haka kuma an haramta taro a dukkanin sassan jihar yayin da zanga-zangar ta shiga rana ta biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan Katsina ta jaddada dokar hana zirga-zirga a fadin jihar yayin da zanga-zanga ta shiga rana ta biyar.
An fara gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis 1 Agusta, 2024 domin nuna adawa da manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar The Sun ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq ne ya jaddada dokar hana fita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za mu kama masu zanga-zanga," Yan Sanda
Rundunar yan sandan Katsina ta ce duk wanda aka kama da saɓa dokar hana fita da sunan zanga-zanga a jihar zai fuskanci fushin hukuma, Punch ta wallafa.
Da ya ke tabbatarwa Legit da ci gaba da hana fitar, ASP Abubakar Sadiq ya ce an sanya 7.00pm-7.00a.m - awanni 12 ke nan a matsayin lokacin da aka hana yawo.
Ya ce ba za su amince a rika karya dokar gwamnati na kokarin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a sassan jihar ba yayin zanga-zanga.
An kafa dokar hana yawo a Katsina
A baya mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Faruq Jobe ya sanya dokar hana fita a karamar hukumar Dutsinma.
Haka kuma ya ce gwamnati ba za ta lamunci gudanar da kowane irin taro a kokarin samar da zaman lafiya.
'Yan sanda sun kama mai zanga zanga
A wani labarin kun ji cewa jami'an 'yan sandan Kano sun cafke matashin da ya ke raba tutar kasar Rasha ga matasa su na dagawa a fadin jihar.
A yau da aka shiga rana ta biyar na zanga-zanga a fadin Najeriya, an gano matasa su na daga tutar kasar Rasha su na neman taimakon Vladimir Putin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng