Ana Tunanin Zanga Zanga Ta Kawo Sauyi a Aso Villa, Tinubu Zai Gana da Hafsoshin Tsaro

Ana Tunanin Zanga Zanga Ta Kawo Sauyi a Aso Villa, Tinubu Zai Gana da Hafsoshin Tsaro

  • An samu canji kan zaman majalisar zartarwa da shugaban kasa Bola Tinubu ya saba yi a ranar Litinin tare da ministocinsa
  • Wasu daga cikin ministocin Bola Tinubu sun halarci taron ba tare da samun bayani kan abin da yasa ba a yi zaman ba a yau Litinin
  • Hakan na zuwa ne yayin da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ke cigaba da gudana a sassan Najeriya musamman a tsakanin matasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta daga zaman majalisar zartarwa da ta saba yi a duka ranar Litinin.

Ana hasashen cewa an dage zaman ne domin tunkarar lamuran tsaro musamman a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Zanga zanga ta birkice, matasa sun toshe hanyoyi

Shugaba Tinubu
An dake zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin ministoci sun taru a dakin taron majalisar zartarwar kafin samun bayani kan cewa an dage zaman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An daga zaman majalisar zartarwa

Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta dage zaman majalisar zartarwar na wannan makon.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu sahihan bayanai kan dalilin dage zaman majalisar ba.

Wasu ministoci sun halarci dakin taro

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wasu daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu sun halarci dakin taron majalisar zartarwar.

Sai dai yayin da suka kammala zama ba tare da ganin shugaban kasa ko mataimakinsa ba suka tattare takardunsu suka tafi.

Za a yi zama na musamman saboda tsaro

Sai dai rahotanni na nuni da cewa a yau ne shugaban kasa zai zauna da hafsosin tsaron Najeriya maimakon zaman majalisar zartarwar.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Duk da barazanar 'yan daba, masu zanga zanga sun sake fitowa

An bayyana cewa shugaban kasa zai zauna da hafsosin tsaro da misalin karfe 2 na rana musamman kan yadda zanga zanga ta barke a Najeriya.

Zanga zanga: CUPP ta tura sako ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da matasa ke cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, kungiyar CUPP ta magantu.

Kungiyar dimokuradiyya ta CUPP ta bayyana babban kuskuren da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a kan zanga zangar da aka fara a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng