Tinubu Ya Yi Magana Kan Masu Kiran Sojoji Su Kwace Mulki, Ya Yi Gargadi

Tinubu Ya Yi Magana Kan Masu Kiran Sojoji Su Kwace Mulki, Ya Yi Gargadi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci matasan Najeriya da kada su bari a yi amfani da su domin kawo cikas ga dimokuraɗiyyar Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya kuma buƙace su da su zo a haɗa ƙarfe da ƙarfe da su domin ciyar da ƙasar nan gaba
  • Shugaban ƙasan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yiwa ƴan Najeriya kan zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi muhimmin kira ga matasan da ke jagorantar zanga-zangar adawa da yunwa da rashin shugabanci na gari a ƙasar nan.

Shugaban ƙasar ya buƙace su da kada su bari maƙiyan dimokuraɗiyya su yi amfani da su wajen kawo cikas ga mulkin dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin farar hula sun fadi kuskuren Tinubu a jawabinsa kan zanga zanga

Tinubu ya ja kunnen matasa
Tinubu ya gargadi matasan Najeriya Hoto: @DefenceInfoNG, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya yiwa ƴan Najeriya jawabi

Shugaban ƙasan ya yi wannan kiran ne a jawabin da ya yiwa ƴan Najeriya kan zanga-zangar da ake yi a ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman na Tinubu sun biyo bayan wasu kiraye-kirayen da masu zanga-zangar ke yi na sojoji su ƙwace mulki a ƙasar nan.

Tinubu ya ce ya gamsu da koke-koken masu zanga-zangar, ya kuma ba su tabbacin cewa manufofinsa na da burin ceto ƙasar nan daga ɓarnar da gwamnatocin baya suka daɗe suna yi.

Tinubu ya ba matasa shawara

Shugaba Tinubu ya buƙaci masu zanga-zangar da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe da su domin ciyar da ƙasar nan gaba, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Tinubu ya yi gargaɗin cewa tattalin arziƙin ƙasar nan ya fara farfaɗowa saboda haka bai kamata a mayar da shi baya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi makudan kudaden da ya ba jihohi domin talaka ya samu sauki

"Tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa, ku taimaka kada ku kawo ƙarshensa. Yanzu da muke jin daɗin mulkin dimouraɗiyya na shekara 25, kada ku bari maƙiyan dimokuraɗiyya su yi amfani da ku."
"Kada ku bari su yi amfani da ku wajen yaɗa wata manufa mara kyau wacce za ta mayar da mu baya a mulkin dimokuraɗiyyar mu."

- Bola Ahmed Tinubu

An faɗi kuskuren Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gamayyar ƙungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun mayar da martani kan jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi dangane zanga-zanga ranar Lahadi.

Gamayyar ƙungiyoyin sun bayyana jawabin na Shugaba Tinubu a matsayin fanko wanda babu komai a cikinsa domin bai kawo mafita kan ƙorafe-ƙorafen ƴan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng