Kungiyoyin Farar Hula Sun Fadi Babban Kuskuren Tinubu a Jawabinsa Kan Zanga Zanga

Kungiyoyin Farar Hula Sun Fadi Babban Kuskuren Tinubu a Jawabinsa Kan Zanga Zanga

  • Jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga-zangar da aƙe yi a faɗin ƙasar nan bai yiwa wasu ƙungiyoyin farar hula ba
  • Gamayyar ƙungiyoyin da ke Katsina sun bayyana cewa shugaban ƙasan bai kawo mafita ba kan ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya suke yi
  • Sun bayyana jawabin na sa a matsayin wanda babu komai a cikinsa domin ya kasa sharewa matasan da suka fito kan tituna hawaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gamayyar ƙungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun mayar da martani kan jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi dangane zanga-zanga ranar Lahadi.

Gamayyar ƙungiyoyin sun bayyana jawabin na Shugaba Tinubu a matsayin fanko wanda babu komai a cikinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan masu kiran sojoji su kwace mulki, ya yi gargadi

Kungiyoyi sun caccaki Tinubu
Tinubu ya yiwa 'yan Najeriya jawabi kan zanga-zanga Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jawabin Tinubu ya bar baya da ƙura

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Kwamared Abdulrahman Abdullahi, ya ce Tinubu bai yi magana ba game da dalilin da ya sa masu zanga-zanga suka fito kan tituna, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa a wajensu, jawabin na shugaban ƙasan tatsuniya ce kawai domin bai ce komai ba dangane da ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya suke da su.

"Matasa suna son a dawo da tallafin man fetur domin sun yi amanna cewa cire shi ne ya haifar da duk matsalar da ake ciki. Amma shugaban ƙasan bai magance wannan koken ba. Hakan na nufin ba shi da shirin dawo da shi."
"Matasa sun ɗauki alluna sun rubuta buƙatunsu, wasu sun rubuta ɓaro-ɓaro cewa 'yunwa', 'a dawo da tallafi'. Amma shugaban ƙasan bai share musu hawaye ba."
"Ya yi magana kan takin da aka ba manoma, amma wane amfani zai yiwa manoma, ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda matsalar rashin tsaro musamman mu a nan yankin Arewa maso Yamma."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ba zai lamunta ba a Najeriya

- Kwamared Abdulrahman Abdullahi

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Tinubu ya fadi kuɗaɗen da ya ba jihohi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana maƙudan kuɗaɗen da ya ba jihohi domin talaka ya samu sauƙi a ƙasar nan.

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fitar da sama da N570bn ga jihohi 36 domin faɗaɗa tallafi ga talakawan ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng