Tinubu Ya Fadi Makudan Kudaden da Ya Ba Jihohi domin Talaka Ya Samu Sauki
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai domin rage wahalhalun da ake sha a ƙasar nan
- Shugaba Tinubu ya ve ya ba jihohi 36 na ƙasar nan sama da N570bn domin faɗaɗa tallafin da ake ba talakawa
- Ya buƙaci matasa da kada su bari a yi amfani da su domin nuna adawa da gwamnatinsa domin ya damu da su matuƙa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana maƙudan kuɗaɗen da ya ba jihohi domin talaka ya samu sauƙi a ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fitar da sama da N570bn ga jihohi 36 domin faɗaɗa tallafi ga talakawan ƙasar nan.
Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi kan zanga-zangar da ake yi a ranar Lahadi, 4 ga watan Agustan 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan Tinubu na rage raɗaɗi a ƙasa
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta damu da matasa inda ta samar da shirye-shirye waɗanda za su amfane su da suka haɗa da rancen ɗalibai, inda ya buƙace su da kada su bari a yi amfani domin nuna adawa ga gwamnati.
Shugaban ƙasan ya nuna cewa ana ci gaba da ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Mun samo $620m a ƙarƙashin shirin samar da sana'o'i ga matasanmu a ɓangaren fasaha na (IDiCE), wanda zai samar da ayyukan yi masu yawa tare da sanya su yin gogayya da takwarorinsu na ƙasashen duniya."
"Haka kuma, mun ba jihohi 36 sama da N570bn domin faɗaɗa tallafi ga mutanen jihohinsu, yayin da sama da masu ƙananan sana'o'i 600,000 suka amfana da tallafinmu. Wasu ƙarin masu ƙananan sana'o'i 400,000 za su amfana."
- Bola Tinubu
Dalilin Tinubu na cire tallafin man fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilinsa na cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen wajen.
Shugaban ƙasan ya ce ya ɗauki matakin cire tallafin man fetur ɗin ne domin ya bunƙasa tattalin arziƙi da kawo ci gaba a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng