Shugaba Tinubu Ya Fadi Abu 1 da ba Zai Lamunta ba a Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana irin Najeriyar da yake son ginawa a lokacin mulkinsa
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ko kaɗan ba zai lamunci ayyukan masu nuna bambancin ƙabilanci ba a ƙasar nan
- Shugaban ƙasan ya ja kunnensu tare da yin gargaɗin cewa doka za ta yi aiki a kan duk wani mai yiwa wata ƙabila barazana a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriyar da yake son ginawa ba ta da wurin nuna bambancin ƙabilanci.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a safiyar Lahadi a Abuja yayin da yake jawabi kan zanga-zangar #Endbadgovernance da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Ya gargaɗi ɓata garin da suka yiwa sauran ƙabilun ƙasar nan barazana da su daina, yana mai cewa doka za ta yi aiki a kansu, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga ta bar baya da ƙura
Zanga-zangar kwanaki 10 da aka shirya, wacce aka fara ranar Alhamis, musamman domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa, ta rikiɗe zuwa tashe-tashen hankula, ɓarnata dukiya da asarar rayuka a sassa da dama na ƙasar nan.
Wasu ɓata gari a kafafen sada zumunta sun buƙaci ƴan ƙabilar Igbo da su fice daga Legas ko su fuskanci zanga-zangar da aka shirya a tsakanin ranakun 20 zuwa 30 ga watan Agustan 2024, cewar rahoton Sahara Reporters.
Masu yin rubuce-rubucen sun kuma umarci ƴan yankin Kudu maso Yamma da ke zaune a yankin Kudu maso Gabas da su dawo gida kafin fara zanga-zangar.
Wane gargaɗi Shugaba Tinubu ya yi
Ana cikin hakan, Shugaba Tinubu ya yi martani kan masu yin waɗannan kiraye-kirayen.
"Ga waɗanda suke amfani da wannan damar domin yin barazana ga wani yanki a ƙasar nan, ku shiga taitayinku."
"Doka za ta yi aiki a kanku. Babu wurin nuna bambancin ƙabilanci ko irin wannan barazanar a Najeriyar da muke son ginawa."
"Dimokuraɗiyyarmu za ta ci gaba ne lokacin da aka kare tare da mutunta ƴancin kowane ɗan Najeriya."
- Bola Tinubu
Tinubu ya shawarci masu zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da su dakatar da ita.
Shugaban ƙasan ya yi kira a gare su da su haƙura su zo a tattauna domin samun mafita kan hanyoyin da za a magance matsalolin da suke kuka da su.
Asali: Legit.ng